Yaƙin Iran: Gwamnatin Nijeriya ta rage harajin shigo da motoci da abinci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta amince da gagarumin rage harajin shigo da kayayyaki kan motoci masu amfani da lantarki, bas-bas na jigilar jama’a, da muhimman kayayyakin da masana’antu ke buƙata, a wani yunƙuri na rage raɗaɗin tsadar rayuwa da kuma tallafa wa harkokin tattalin arziki.

Wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na rage matsin tattalin arziki da ke ƙaruwa sakamakon tashin farashin mai a kasuwannin duniya, wanda rikicin siyasa tsakanin ƙasashe ya haddasa.

An amince da wannan tsari ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin wani ɓangare na manyan tsare-tsaren kuɗi da nufin kare tattalin arzikin Nijeriya daga illolin rikicin Gabas ta Tsakiya.

Mataimaki na musamman ga Shugaban ƙasa, Dada Olusegun, shi ne ya bayyana cikakkun bayanai, inda ya ce rage harajin zai taimaka wajen rage hauhawar farashi, sauƙaƙa sayayya ga jama’a, da kuma ƙarfafa kasuwancin cikin gida.

A ƙarƙashin sabon tsarin, an cire harajin shigo da motoci masu amfani da lantarki (EVs) da bas-bas na sufuri gaba ɗaya daga kashi 5 zuwa sifili, wanda ake sa ran zai rage tsadar sufuri tare da ƙarfafa amfani da hanyoyin sufuri masu tsafta.

Haka kuma, gwamnati ta soke harajin kashi 5 kan injunan masana’antu, domin rage kuɗin samarwa da ƙara aarfafa masana’antu.

A ɓangaren sauran kayayyaki kuwa, an rage harajin motocin hawa daga kashi 70 zuwa 40, yayin da na shinkafa ya sauka daga 70 zuwa 47.5 ga cikakkiyar shinkafa, da kuma zuwa 30%l ga wacce aka kakkarya. Haka kuma an rage na sukari da sauran kayayyakin masarufi.

A ɓangaren gine-gine da masana’antu, an rage harajin ƙarafa da tayal, matakin da ake sa ran zai rage tsadar gini da samar da kayayyaki.

Gwamnati ta kuma tanadi wa’adin kwanaki 90 daga ranar 1 ga Afrilu domin bai wa kasuwanni damar daidaitawa da sabon tsarin, tare da kaucewa tangarɗa a farashi ko wadatar kaya.

Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Isra’ila, Amurka da Iran ke haifar da rikice-rikicen kasuwar mai ta duniya, musamman a mashigar Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci wajen safarar mai.

Farashin mai a Nijeriya ya kai kusan naira 1,350 kowace lita a ‘yan kwanakin nan, sakamakon tashin farashin mai a duniya da kuma tsadar jigilar kaya.

A wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya umarci Ma’aikatar Kuɗi da Tsare-tsaren Kasafi tare da Babban Jami’in Ayyukan Gwamnati su samar da hanyoyin rage wahalar rayuwa ga jama’a.

Masana tattalin arziki sun bayyana wannan mataki a matsayin mai amfani a gajeren lokaci wajen rage hauhawar farashi, amma sun jaddada buƙatar ƙarin gyare-gyare. Shugaban Centre for the Promotion of Private Enterprise, Muda Yusuf, ya ce wannan tsari zai rage kuɗin samar da kayayyaki tare da ƙara ƙarfafa gasa a kasuwa.

Sai dai ya yi gargaɗi cewa dole ne a kula wajen rage harajin abinci domin kada hakan ya cutar da manoma na cikin gida. Haka kuma, masaniyar sufuri, Aisha Suleiman, ta ce wannan tsari na iya rage dogaro da man fetur idan aka samar da ingantaccen tsarin cajin lantarki.

A nasa ɓangaren, masanin manufofin kuɗi, Ken Ife, ya yi gargaɗin cewa gwamnati na iya fuskantar raguwar kuɗaɗen shiga na ɗan lokaci saboda rage harajin shigo da kayayyaki.

Duk da haka, wannan mataki na nuna yadda gwamnati ke ƙoƙarin amfani da dabarun kuɗi domin kare tattalin arziki da kuma tallafa wa jama’a a wannan lokaci mai cike da ƙalubale a duniya.

By ukarofi