Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rikicin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Amurka da Isra’ila a gefe guda da Iran a ɗaya ɓangaren ya fara nuna mummunan tasiri a kan tattalin arzikin Nijeriya, inda ya haddasa tashin gwauron zabi a farashin fetur, hauhawar kuɗin sufuri da kuma tsadar rayuwa gaba ɗaya.
Wannan rikici, wanda ya ɓarke a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, ya sauya daga rikicin wakilai zuwa cikakken yaƙi kai tsaye. An fara shi ne da hare-haren sama na haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar, wanda suka sanya wa suna “Operation Epic Fury” da “Operation Roaring Lion”.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana hare-haren a matsayin wani mataki na kawar da barazana da lalata ƙarfin makaman nukiliyar Iran.
Ko da yake an samu tsagaita wuta na ɗan lokaci, rikicin bai tsaya ba, yayin da ake ci gaba da musayar hare-haren makamai masu linzami.
Rufe mashigar ruwan Hormuz ya jawo tashin farashin mai a duniya zuwa sama da dala 100 kan ganga, lamarin da ya girgiza tsarin samar da mai a duniya.
A Nijeriya, inda tattalin arziki ya dogara da man fetur, wannan ya jawo tashin farashin mai zuwa tsakanin N1,300 zuwa N1,370 a kowace lita, yayin da a kasuwar bayan fage farashin ya kai har N2,500 a wasu yankuna. Wannan ya haifar da tsananin wahala ga jama’a, musamman ta fuskar sufuri da abinci.
Wata ma’aikaciyar kamfani mai zaman kansa a Abuja, Joana Ade, ta bayyana halin da take ciki, tana mai cewa kuɗin sufuri da take kashewa sun ninka fiye da yadda take biya a baya. Ta ce maimakon ajiya, yanzu ma’aikata na faɗawa cikin bashi saboda ƙarancin albashi da tsadar rayuwa.
Sai dai wasu ’yan ƙasa na ganin wannan lokaci ne na sake tsari. Wani ma’aikacin gwamnati, Ezekiel Chukwu, ya ce ya kamata mutane su rage zirga-zirga, su yi aiki daga gida inda zai yiwu, tare da fifita muhimman buƙatunsu domin rage tasirin wahalar.
Direbobin tasi ma ba su tsira ba. Wani direba a Abuja, Ibrahim Danlami, ya ce yana kashe sama da N50,000 a rana wajen sayen mai, amma har yanzu ba ya samun riba saboda yawan fasinjojin da ke roƙon rangwame. Ya ce halin da ake ciki ya sa kowa ke ƙoƙarin taimakon juna saboda tsananin matsin rayuwa.
Haka kuma, ’yan kasuwar mai sun bayyana cewa suna fama da ƙarancin saye, domin mutane da dama sun ajiye motocinsu suna komawa amfani da sufuri na haya. Wani dillalin mai, Aliyu Muhammad, ya ce sayar da mai ya ragu sosai duk da tsadar da ake sayen shi daga kasuwa.
Duk da haka, ana ganin wannan rikici ya ƙara haskaka muhimmancin matatar mai ta Dangote, wadda ke taimakawa wajen rage giɓi a kasuwar mai ta nahiyar Afirka.
A ƙarshe, masana na ganin cewa mafita na dogon lokaci ita ce samar da hanyoyin da za su rage dogaro da ƙasashen waje, tare da inganta tattalin arzikin cikin gida domin jure irin wannan girgiza daga ƙasashen waje.
