Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta buƙaci a riƙa mutunta shari’a a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Duniya (IHRC-RFT) a Nijeriya ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun ƙaruwar amfani da umarnin kotu wajen ƙauce wa shari’a bayan aikata laifuka ko tauye haƙƙin mutane inda take neman a riƙa mutunta shari’a a ƙasar.

ƙungiyar ta lura cewa amfani da umarnin kotu a Nijeriya wajen ba bisa ƙa’ida ba na neman ya zama ruwan dare wanda ke hana jami’an tsaro daga kama ko binciken masu aikata laifi.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da daraktan ƙasa ta ƙungiyar Amb. Abdullahi Bakoji Adamu ya fitar.

Sanarwar ta ce, wannan dabi’a tana barazana ga amincin tsarin shari’a kuma tana rage ikon jami’an tsaro wajen gudanar da aikinsu.

IHRC-RFT ta bayyana cewa ba ta kira a hana umarnin kotu ba. Sai dai tana buƙatar a tabbatar cewa shari’a da adalci da gaskiya su ne ke jagorantar yadda ake bayar da irin waɗannan umarni, domin kada wani ya yi amfani da dokoki wajen tauye haƙƙin wasu.

“Amfani da tsarin shari’a ba bisa ƙa’ida ba ya saɓa wa dokokin kare haƙƙin ɗan adam na ƙasa da ƙasa wadda ta tanadi cewa kowa yana da daidaito a gaban doka da samun kariya ba tare da bambanci ba.

A matsayin wani ɓangare na yaƙin neman adalci, IHRC-RFT ta aike da wasiƙu ga ministan shari’a da babban lauyan tarayya da kuma babban alƙalin Nijeriya, tana kira da su su gudanar da bincike da duba yadda ake amfani da umarnin kotu a aasar.

ƙungiyar ta kuma buƙaci su ƙarfafa hanyoyin da ke tabbatar da cewa umarnin kotu ba za su zama kayan toshe shari’a ba sannan su haɗa kai da ɓangaren majalisa da na shari’a da na zartarwa da jami’an tsaro domin tabbatar da tsarkake tsarin shari’ar Nijeriya bisa ƙa’idojin kare haƙƙin ɗan adam na duniya.

By ukarofi