Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki tsare-tsaren tattalin arziƙin shugaba Tinubu tare da kafa hujja da rahoton bankin duniya wanda ya ce talauci na ci gaba da tsananta a Nijeriya.
A cikin jawabin da ya fitar a ranar Juma’a a Abuja, mai taimaka wa Atiku kan yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya ce, bankin duniyar ya nuna irin “mahuyacin halin” da miliyoyin ‘yan Nijeriya ke fama da ita.
Ya abato bankin na cewa sama da kaso 60% na ‘yan Nijeriya na rayuwa ƙasa da ma’aunin talauci idan aka kwatanta da kaso 40% da suke fama da talauci a shekarun baya, yana mai bayyana irin koma bayan da aka samu.
Bankin duniya a cikin rahoton da ta fitar na baya-bayan nan a watan Afirilun 2026 mai taken, “Lallai ne goben Nijeriya ya fara a yau: Nazari kan irin ci gaban kananan yara”, ta ce, talauci ya ƙara tsananta sosai duk da irin ci gaban da aka samu.
Rahoton, wanda aka fitar da shi a Abuja a ranar Talata, ya nuna cewa talauci ya ƙaru a Nijeriya da kaso 63% a shekarar 2025, kuma ya shafi ‘yan Nijeriya miliyan 140. Bankin ya ce ya lura da cewa duk da cewa an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki, akwai bambancin tsakanin jin hakan a kanun labarai da kuma yadda rayuwar al’umma ta yau da kullum ta sauya.
A cewar rahoton, talauci ya ƙaru a cikin shekarun bayan nan daga kaso 56% a 2023 zuwa kaso 61% a 2024, kafin daga bisani ya dawo kaso 63% a shekarar 2025.
Wannan yanayi a cewar bankin, ya nuna yadda al’umma masu ƙaramin ƙarfi ke fafutukar rayuwa da ƙalubalen tattalin arziƙi da rashin daidaito wajen rabon arzikin ƙasa.
Bankin duniyar ya yi gargaɗin cewa a yayin da ake ta aiwatar da tsare-tsaren daidaita tattalin arziƙin a cikin waɗannan lokuta, tasirinsu na ƙaramin zango na ci gaba da dukan masu ƙaramin ƙarfi musamman rashin tsarin ingantacce na ba su kariya.
A yayin da yake magana kan ƙaruwar tsananin talauci, Atiku ya ce ba wai abu ne da ya faru kwatsam ba, ya ce abu ne da ya shafi aiwatar da munanan tsare-tsare.
Ya soki irin yadda kwatsam aka cire tallafin man fetur da kuma karya darajar Naira, yana mai cewa an ɗauki duk waɗannan matakai ne ba tare da fidda wata hanya ta kare al’ummar Nijeriya ba.
A cewarsa, tasirin hakan a fili yake a dukkan sassan ƙasar idan aka kalli hauhauwar farashin abinci da ƙaruwar kuɗin sayen makamashi da rufe sana’o’i.
“A yayin da gwamnatin Tinubu ke cewa an samu bunƙasar matsakaicin tattalin arziƙi, ‘Yan Nijeriya na ci gaba da rayuwa cikin tsanani – fama da yunwa da rashin tabbas da kokawar yadda za su rayu a kullum,” ya faɗa.
Ya ƙara da cewa sauye-sauyen da gwamnatin ke kawowa “sun girgiza tattalin arziƙin marasa ƙarfi” wanda suke kira da waraka.
Ya ce rahoton bankin duniyar ya fallasa giɓin da ke tsakanin ikirarin ngwamnati na kawo wa al’umma ci gaba da kuma zahirin rayuwar da talakawa ke ciki.
Atiku ya haska cewa akwai buƙatar rungumar tsare-tsare masu tasiri da kuma bi sannu a hankali tare da kawo tsarin da zai shinge al’umma daga raɗaɗi.
Ya ce sauye-sauyen ya kamata su haɗa da samar da ayyukan yi da samar da wadataccen abinci da kuɗin shiga da tallafa wa ƙananun sana’o’i da noma da masana’antu.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya yi kira kan daidaita harkar kuɗi da kuma sake dawowa da masu zuba hannun jari ƙarfin guiwarsu a kan Nijeriya.
Atiku ya yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da tafiya a kan waɗannan tsare-tsare, za a ci gaba da fama da taɓarɓarewar tattalin arziƙi.
“Shugabanci ba maganar rufe gazawar ba ne, magana ce ta gyara,” ya faɗa, inda ya ƙara da cewa ƙasar nan na da zaɓi biyu ne ko dai a ci gaba da zama cikin mawuyacin hali ko kuma a gyara tsare-tsare da za su dawo wa da kowa yalwar arziƙi.
