
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta umarci a saki Sheikh Sani Abdulƙadir Zaria, sannan a biya shi diyyar Naira miliyan 5 na dameji bisa tauye masa ‘yanci da dokar ƙasa ta ba shi da hukumomin tsaro da wani bankin kasuwanci suka yi.
A yayin shari’ar, wadda Mai Shari’a Peter O. Lifu ya jagoranta, ya bayyana cewa riƙe Shehin malamin na tsawon lokaci ba tare da izinin kotu ba, tauye masa ‘yancin kare masa mutunci, walwala, adalcin sauraro da zirga-zirga ne, waɗanda sun ci karo da hukuncin dokar ƙasa ta 1999 da kuma ta kare ‘yancin al’ummar Afirka.
A cewar takardar ƙarar mai lamba kamar haka FHC/ABJ/CS/55/2026 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, shehin ya shigar da ɓangarori biyar ƙara da suka haɗa da hukumar EFCC, DIA, Antoni Janar na Ƙasa, Bankin Ja’iz da kuma hukumar SSS.
Mai Shari’ar ya umarci Antoni Janar a matsayinsa na shugaban lamuran doka, da ya tabbatar an kiyaye dukkan umarnin da kotun ta bayar akan al’amarin.
Haka kuma, kotun ta umarci a gaggauta sako malamin ba tare da gabatar da wani sharaɗi ba.
Kazalika, ta ayyana dakatar da hada-hadar kuɗaɗe a asusunsa da Ja’iz ya yi ba tare da izinin kotu ba a matsayin abin da aka yi ba bisa doka ba da ke nuna tauye masa ‘yanci. Akan haka ne alƙalin ya umarci EFCC da bankin kowannensu ya biya malamin diyyar Naira miliyan 1.
Bugu da ƙari, Mai Shari’a Lifu ya umarci DIA da SSS da su biya diyyar miliyan N4 ga malamin akan tauye masa ‘yanci.
