Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da fara biyan sabon tsarin albashi na Hakimai da ke faɗin jihar tare da kira ga hukumar kula da ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar da ta gaggauta basu takardar kama aiki da zai taimaka masu wajen fara biyan su albashin.
Sabon tsarin albashi ya kai hakiman da magadan a matakin albashi na 16 wanda yayi daidai da muƙamin daraktan a gwamnati,sai kuma magadai da aka ɗaga su a matakin albashi zuwa GL 10.
Gwamnan ya bayyana dokar masarautu ta 2025, wani muhimmin mataki da ke nuna ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa cibiyoyin gargajiya, inganta tsaro da inganta shugabanci a faɗin jihar.
Da yake jawabi a wajen bikin da aka gudanar a fadar gwamnatin Katsina, Gwamna Raɗɗa ya bayyana dokar masarautu ta 2025 a matsayin wata sabuwar hanya da za ta ƙarfafa ayyuka, nauyi da tsarin gudanar da majalisun masarautu.
Ya jaddada cewa dokar ta samo asali ne daga tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki, ciki har da sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da masana harkokin siyasa da mulki.
A wani ɓangare na aiwatar da dokar, Gwamnan ya miƙa takardun ƙara darajar sarauta ga sarakunan da aka ɗaukaka a masarautu daban-daban na masarautar Daura da Katsina.
Ya bayyana cewa ɗaukakar ta dogara ne da cancanta, hidima da kuma buƙatun zamani na shugabanci a matakin ƙasa, tare da kiyaye al’adun al’umma.
Haka kuma, Gwamna Raɗɗa ya amince da biyan sabon tsarin albashi ga sarakunan gargajiya da ma’aikatan majalisun masarautu. Wannan sabon tsari na da nufin inganta walwala, ƙara ƙwazo, inganta tsaro da kuma tabbatar da cewa cibiyoyin gargajiya sun samu isasshen tallafi don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Da yake jawabi a wajan taron, mai ba gwamna shawara kan harkokin masarautu Alhaji Usman Abba Jaye, ya bayyana muhimmancin wannan sauyi, inda ya ce dokar ta samar da ingantaccen tsari na doka da gudanarwa ga masarautu a jihar.
Ya yaba wa gwamnan bisa hangen nesa da jajircewarsa wajen ƙarfafa cibiyoyi, yana mai cewa sabon tsarin albashi zai ƙara himma da ƙwazon masu riƙe da sarautu.
Sai ya buƙaci sarakunan da aka ɗaukaka su tabbatar da sun cika amana ta hanyar adalci, gaskiya da hidima ga al’umma.
A jawabinsa, shugaban hukumar kula da ma’aikatan ƙananan hukumomi ya jaddada cewa wannan gyara zai ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙananan hukumomi da cibiyoyin gargajiya.
Ya bayyana sabon tsarin albashin a matsayin mataki mai dacewa da zai ƙarfafa wa ma’aikata da inganta ayyuka a matakin ƙasa, tare da tabbatar da goyon bayan hukumar wajen aiwatar da dokar yadda ya kamata.
A madadin masarautun Daura da Katsina Kauran Katsina, Alhaji Aminu Nuhu Abdulkadir, ya bayyana godiya ga Gwamnan bisa wannan muhimmin tsari. Ya bayyana dokar a matsayin mai amfani kuma da hangen nesa, tare da tabbatar da cikakken goyon baya da haɗin kai na masarautu wajen tabbatar da nasarar aiwatar da tsare-tsaren gwamnati.
