Dagacin Bomala ya naɗa Lawan Siraka Turakin Bomala

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Dagacin Bomala da ke mazaɓar Garko a ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, Malam Dauda Adamu, ya naɗa Lawan Siraka, wanda aka fi sani da Baba Lawan, a matsayin Turakin Bomala, a wani biki mai kayatarwa da ya samu halartar jama’a daga sassa daban-daban.

Da yake jawabi a madadin abokan sabon Turakin, Muhammad A. Barde, ya yabawa Dagacin bisa ganin cancantar Baba Lawan da ya ba shi wannan mukami, yana mai cewa mutum ne mai son zaman lafiya wanda bai taba shiga rikici da kowa ba tun bayan zuwansa Bomala fiye da shekaru 20 da suka wuce.

Ya ƙara da cewa Baba Lawan ya bayar da gudummawa sosai wajen cigaban al’umma, wanda hakan ya sa aka karrama shi da wannan sarauta, tare da bayyana cewa zai ci gaba da hidimtawa jama’a yadda ya saba.

A nasa ɓangaren, Mai Unguwar Bomala, Malam Ali Bomala, ya jinjinawa Dagacin kan yadda yake ƙoƙarin bunƙasa masarautar ta hanyar zaɓo mutanen kirki da basu mukaman sarauta. Ya bayyana sabon Turakin a matsayin dattijo mai mutunci da kowa ke girmamawa.

Shi ma Usman Siraka, wanda ya gabatar da tarihin Baba Lawan, ya ce an haife shi a unguwar Kumbiya-kumbiya a Gombe, daga bisani iyalinsa suka koma Bolari kafin ya zauna a Bomala. Ya kara da cewa ya yi karatun addini inda ya samu difloma a Kwalejin Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Kwaine.

A jawabinsa, Dagacin Bomala, Malam Dauda Adamu, ya bayyana cewa nadin Baba Lawan ya biyo bayan irin kokari da sadaukarwar da yake yi wa al’umma. 

Ya ce duk da cewa magabacinsa ne ya fara ba shi mukamin kafin rasuwarsa, amma ya gamsu da yadda ya nuna kwarewa da jajircewa.

Ya kuma yi kira ga sauran masu rike da sarauta da su hada kai tare da bada gudummawa wajen cigaban masarautar.

Bikin naɗin ya samu halartar ‘yan uwa da abokan arziki daga sassa daban-daban na jihar Gombe, da kuma wasu baki daga karamar hukumar Gwaram a jihar Bauchi, inda suka halarta domin taya sabon Turakin murna da nuna goyon baya.

By ukarofi