Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar inganta noman rani(KTIDA) ƙarƙashin jagorancin Eng. Salim Sulaiman Maiadua ta fara aikin gina rijiyoyin noman rani a wasu ƙananan hukumomi a jihar Katsina.
An fara aikin a ƙananan hukumomin Daura, Kaita, Funtua da Malumfashi, aikin gina rijiyoyin ya fara nisa inda ake cigaba da tabbatar da dukkanin ayyukan sun gudana a yadda ya kamata domin amfanin manoman rani a yankunan baki ɗaya.
Babban manufar wannan aiki ita ce ƙara ƙarfin ban-ruwa, inganta samun ruwa domin ayyukan noma, tare da tallafa wa manoma su riƙa yin noma a duk tsawon shekara a al’ummomin da za su amfana.
Rahotannin farko daga wuraren aikin sun nuna cewa ana samun gagarumin ci gaba, inda ake gudanar da aikin hako rijiyoyin bisa ƙa’idoji da ƙayyadaddun sharuɗɗan da ya dace.
Hukumar tana ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da kammala aikin a kan lokaci yayin da aikin ke shiga matakai na gaba.
