Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Dan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya ƙaddamar da ɗora harsashin gina cibiyar kula da lafiya a matakin farko a unguwar Shararrar Pipe da ke cikin birnin Katsina.
An kaddamar da aikin ginin a unguwar Danbedi da ke cikin garin Katsina, ƙarƙashin jagorancin Hon. Sani Aliyu Danlami.
Da yake jawabi jim kaɗan da ƙaddamar a fara aikin , Hon. Sani Aliyu Danlami ya bayyana cewa “munyi tunanin samar da asibitin a wannan wuri ne saboda yadda yake a matsayin Tafki a da, amma gwamnatin Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta cike shi ya zama fili,”Inji Danlami.
“Wannan yasa bisa kwaikwayon ayyukan Mallam Dikko Umar Raɗɗa, da muke yi yasa muka ga dacewar mayar da wurin asibiti domin ci gaban al’umma,”Inji ɗan majalisar.
Ya kuma bayyana cewa an fara gudanar da aikin, kuma ana sa ran kammala shi nan ba da jimawa ba domin amfanin al’umma baki ɗaya.
Taron ya samu halartar Shugaban karamar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad (AD Saude), tare da sauran masu ruwa da tsaki da al’umma.
