
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An hanzarta fitar da Shugaba Donald Trump daga dandamali yayin da aka ƙaddamar da wasu harbe-harbe a taron cin abincin wakilan Fadar White House.
Trump ya ce, wani da ake zargin ɗan bindiga ne da makamai da dama ya kutsa wa shingen binciken jami’an tsaro kana ya fara harbe-harbe a wajen taron.
An ruwaito cewa, an ɗauke Trump da sauran jami’an gwamnati da ke wajen cikin aminci.
Sannan, wanda ake zargin, wanda a yanzu yake hannun hukuma, za a gurfanar da shi bisa tuhumar sa da laifin amfani da bindiga yayin tarzoma da kuma cin zarafin jami’in gwamnatin tarayya ta hanyar amfani da makami mai haɗari, kamar yadda babban lauyan Gundumar Columbia, Jeanine Pirro ya bayyana.
Ana zargin wani ɗan Jihar Kalifoniya mai kimamin shekaru 31 da hannu a laifin, a rahoton hukumomi ga CNN.
Haka kuma, an harbi wani jami’in leƙen asiri da ke sanye da rigar kariya, wanda tuni aka garzaya da shi asibiti.


