Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Jos
Wata muhawara ta kaure a zaurukan sada zumunta tsakanin wasu ƴan Nijeriya, musamman ƴan kudancin ƙasar nan, waɗanda ke bayyana ra’ayoyinsu game da wani rahoto na musamman da wata jaridar Turanci ta ƙasar Amurka da ake kira The New York Times ta wallafa, wanda ke bayyana yadda wasu mata ƴan Arewacin Nijeriya suke cin karen su babu babbaka a manhajar WhatsApp ta hanyar sayar da littattafansu masu ɗauke da rubutun batsa.
Wata ƴar jarida mai suna Ruth Maclean da taimakon abokin aikinta ɗan Nijeriya Isma’il Auwal sun gudanar da wani bincike game da zaurukan marubuta na mata zalla da ake buɗe wa a WhatsApp da sunan tallan littattafan Hausa na batsa da ake rubutawa ana yaɗawa gaɓa-gaɓa, don masu karatu, waɗanda aka ce akasarin su matan aure ne.
Jaridar ta samu kutsawa wani daga cikin irin waɗannan zauruka da aka yi wa taken Oum Hairan World wanda ta gano akwai dubban mata dake bibiyar littattafan marubuciyar mai suna Fauziyya Tasi’u Umar mai laƙabi da Oum Hairan ƴar shekaru 31, wacce ita ce ta buɗe wannan zauren. Mata na biyan aƙalla Naira 300 a zauren gama-gari don karanta littafin marubuciyar, bayan sun bibiyi shafukan kyauta na gabatarwar littafin da ake fitarwa don jan ra’ayin masu karatu. Yayin da marubuciyar kan sanya sanarwar cewa, duk masu sha’awar a ware su zuwa zaure na musamman (ɓ-ɓIP) za su biya Naira 1500 ta asusun bankin marubuciyar. Sanadiyyar wannan kasuwanci dai ba ƙaramin kuɗi marubuciyar ke samu ba, saboda yadda matan ke zumuɗin karanta littattafan nata.
A cewar jaridar, a baya dai an ga yadda marubuta littattafan soyayya na Hausa suka riƙa fuskantar ƙalubale daga hukumomi ƙarƙashin Hukumar Tace Finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano wacce ta riƙa ƙwace wasu littattafan da ake bugawa waɗanda Hukumar ke ganin labaran da ke ƙunshe a cikin su suna iya lalata tarbiyya. Har ma a wani lokaci an riƙa taron ƙona irin waɗannan littattafai, sakamakon tsarin shari’ar Musulunci da Jihar Kano ke amfani da shi. Sai gashi a wannan lokaci sanadiyyar ɓullar manhajojin sadarwa na zamani, marubuta littattafan batsa sun ƙara yawa da samun karɓuwa, saboda yadda suke fitar da littattafansu daki-daki, ba tare da sa’idon hukumomi ba, waɗanda hankalinsu ya fi komawa kan littattafan da ake wallafawa. Kodayake Oum Hairan ta shaidawa jaridar The New York Times cewa, Hukumar Hisba ta Kano ta taɓa gayyatar ta zuwa ofishin su, inda suka yi mata nasiha game da littattafan da take rubutawa, wanda ita kuma a cewarta ta sanar da su tana yi ne don matan aure, kuma tana ƙoƙarin tabbatar da ganin babu budurwa ko wacce ba ta da aure a cikin zaurukan da take buɗewa, domin ita ma tana da yara da take ƙoƙarin kiyaye tarbiyyar su.
Rahoton bai nuna matakin da Hukumar Hisbah ta ɗauka akan marubuciyar ba, in ban da nasihar da suka yi mata kan ta rage amfani da kalmomin batsa da take sanyawa ba, waɗanda malaman hukumar ke ganin sun yi tsauri sosai. Ita kuwa Oum Hairan, wacce ta ce ba ta tsoron wani ya san asalin ko ita wacece, waɗannan kalmomi na batsa da bayanan yadda mata da miji ke saduwa da juna, su ne suke jan hankalin masu bibiyar littattafan ta.
Bayan Oum Hairan, jaridar ta samu zantawa da wasu marubutan batsan waɗanda su kuma ke fargabar a san asalin su, kasancewar su Hausawa Musulmi, kuma ƴan’uwan juna. Oum Aphnan da Maman Teddy, waɗanda ke ganin saƙonnin da suke isarwa sun fi saurin shiga ta irin wannan salon, saboda yadda masu sha’awar littattafan ke jin daɗin irin batsar da ake sanyawa.
Fitar wannan rahoto dai ya jawo muhawara sosai, daga masu karatu, da suka haɗa har da Turawa da ƴan kudancin Nijeriya, waɗanda ke yabawa da nuna farincikinsu da yadda waɗannan mata marubuta ke nuna bijirewa ga tsauraran dokokin shari’a da al’adun Hausawa. Sai dai a wajen marubutan adabin Hausa da suke ƙalubalantar irin wannan salon rubutu, wanda suka ce yana ɓata musu suna da kimarsu a idon mutane, fitar wannan rahoto abin kunya ne gare su.
Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino, shi ne Sarkin Mawallafan Arewa, kuma jagora a tsakanin marubutan adabi, ya bayyana cewa. ‘Rubutu kamar shuka ce wacce duk wanda ya shuka za ta tsiro kuma mutum ya girbi abin da ya shuka har ma ya ci ƴaƴanta. In ka rubuta mai kyau to, ka shuka abu mai kyau, idan ka rubuta marar kyau shi ma kamar ka shuka marar kyau ne. Saboda haka, duk abin da mutum ya shuka shi zai girba, ko a kansa ko akan ƴaƴansa ko wani nasa, ko ma dai akan al’umma. Don haka su masu rubutun batsa da suke yi don su samu kuɗi ko ɗaukaka, abin da suke mantawa shi ne, in babu mutuwa da akwai tsufa! Lokaci na zuwa da idan ka yi wani rubutu marar kyau bayan wasu shekaru idan aka zo aka karanta a gaban ƴaƴanka ko jikokinka abin ba zai maka kyau ba. Haka kuma ko mutuwa ka yi idan aka fito da abin da ka rubuta, sai an yi maka addu’a daidai da abin da ka rubuta.’
Shi kuwa a nasa ɓangaren, Bamai Dabuwa, jigo a zauren marubuta na manhajar WhatsApp ya ɗora alhakin abubuwan da ke janyo ƙaruwar marubutan batsa kan lalacewar tarbiyyar al’umma, inda ya ce marubuci yana kallon rayuwar al’umma ne sai ya yi rubutu akai. Don haka idan tarbiyyar al’umma ta lalace to, wannan hoton marubuci zai ɗauka ya yi nazari akai. Sannan a halin da ake ciki marubutan Hausa na fuskantar ƙalubale babba na rashin masu karatu, saboda komabaya da ake fuskanta ta rashin son karatu a wajen Hausawa, in dai ba akwai wani abu da ya ja hankalin su ba. A cewarsa, wannan na daga cikin dalilan da suke angiza wasu marubutan zuwa ga rubutun batsa, don samun mabiya da neman kuɗi.
Sai dai Bamai ya ƙalubalanci iyaye, da malamai da su himmatu wajen faɗakar da al’umma muhimmancin riƙo da koyarwar addini da gyaran tarbiyya, ta haka ne za a samu damar kawar da tunanin mutane kan mu’amala da abubuwan batsa, har su ma marubutan su rasa mabiya, a dawo kan turbar da ta dace. Ya shawarci marubuta su kiyaye martabar kansu da ta addininsu, su tsaftace rubutunsu don al’umma ta amfana da rubutunsu.
Hassana Suleiman Isma’il, da aka fi sani da Sanah Matazu ita ce shugabar ƙungiyar mata marubuta ta Women of Words, ta ce rubutun batsa aiki ne na marasa kunya da tarbiyya, duk da yake masu yin wannan salon rubutun suna ganin suna yin haka ne don gyara zamantakewar aure. Sai dai ta ce, ai addinin Musulunci ya koyar da al’ummar musulmi yadda za su yi kowacce irin rayuwa, ba tare da sun zubar da kunyar su sai ta fuskar batsa ba. Rubutun batsa ba shi da wani alfanu ga al’umma, kuma hatta masu irin rubutun ba su da kima a cikin jama’a.
Hadiza Ibrahim D. Auta, wata fitacciyar marubuciyar onlayin ce da take ganin neman kuɗi da mabiya ne yake sa wasu marubutan shiga rubutun batsa. Wasu kuma masu karatun ne suke zuga su kan cewa, idan ana saka batsa littafin ya fi daɗin karatu. Hakan ne yake ƙara musu ƙaimi wajen zage damtse suna karta rashin ɗa’a, babu kunya babu tsoron mutuwa da haɗuwa da Ubangiji a ranar lahira.
