Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai hari wani rukunin gidajen sojoji a Abuja, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya tare da jikkatar wasu.
Rahotanni sun ce an kai harin ne a ranar Alhamis, 30 ga Afrilu, 2026, a Army Post Serɓice Housing Estate da ke Kurudu, a Babban Birnin Tarayya (FCT).
A cewar majiyoyi, ‘yan bindigar kimanin bakwai ne suka kutsa cikin wani gida a cikin rukunin gidajen da nufin sace wani mazaunin gidan.
Sai dai maƙwabta sun yi gaggawar kai rahoto ga jami’an tsaro, lamarin da ya sa sojojin da ke gadin yankin suka yi saurin kai ɗauki.
An ce haɗin gwiwar sojoji da ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Kurudu sun fatattaki maharan tare da dakile yunƙurin satar da kuma fashi a Army Post Serɓice Housing Estate (Phase 5).
A yayin musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da maharan, an kashe ɗaya daga cikin ‘yan bindigar, yayin da wani ya tsere da raunukan harbin bindiga, sauran kuma suka tsere ta bayan rukunin gidajen cikin ruɗani.
Rahotanni sun kuma nuna cewa wanda maharan ke son sacewa wani fitaccen attajiri ne da ke zaune a cikin rukunin gidajen.
Majiyoyi sun ce lamarin ya janyo fargaba a tsakanin mazauna yankin, duk da cewa jami’an tsaro sun dawo da doka da oda cikin gaggawa bayan harin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Abuja ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin.
Sai dai ana sa ran hukumomin tsaro za su ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin domin hana aukuwar irin wannan lamari a gaba.
