2027: Kar ku wargaza APC saboda burinku — Shettima ga masu neman takara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Sanata Kashim Shettima, ya yi gargaɗi ga masu neman tikitin takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC da kada su rusa jam’iyyar idan ba su samu nasara ba a zaɓen fidda gwani gabanin babban zaɓen 2027.

A cikin wani rubutu mai taken “2027: Kar ku rushe rufin gida”, Shettima ya ja hankalin ’yan jam’iyyar da masu neman takara da su guji barin burin siyasa ko saɓanin ra’ayi ya haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar.

Ya amince cewa saɓanin buri, yankuna, goyon bayan magoya baya da lissafin siyasa abu ne na ɗabi’a a irin wannan lokaci, amma ya jaddada cewa dukkan ’yan APC suna cikin gida ɗaya. “Mu duka ’yan gida ɗaya ne a siyasa,” inji shi.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi gargaɗi ga shugabanni da mambobin jam’iyyar da kada su bari kafafen yɗɗa labarai ko masu neman tayar da fitina su yi amfani da su wajen haddasa rikici.

“Akwai waɗanda za su riƙa raɗa cewa an tauye wani ɓangare ko an ware wasu, amma waɗannan dabaru ne na siyasa domin haddasa rikici kafin a fara fafatawa,” inji shi.

Ya ƙara da cewa jagoranci na gaskiya na buƙatar a kauce wa irin waɗannan tayar da hankali, tare da mayar da hankali wajen kiyaye haɗin kan jam’iyya.

Shettima ya bayyana cewa a siyasa, mutum ɗaya ne kaɗai zai zama ɗan takarar jam’iyya a ƙarshe, duk da cewa mutane da dama za su yi ƙoƙari da kashe kuɗi domin cimma burinsu.

“Wannan shi ne lissafin dimokuraɗiyya. Duk da wahala, ba lallai ba ne sakamakon ya zama rashin adalci,” inji shi.

Ya jaddada cewa ainihin halayen ɗan siyasa suna bayyana ne lokacin da ya fuskanci rashin nasara, yana mai cewa nasara kowa na iya murna da ita, amma ɗaukar rashin nasara da haƙuri shi ne ainihin gwaji.

Dangane da batun goyon baya da ke haifar da cece-kuce a cikin jam’iyyar, Shettima ya ce irin wannan ba sabon abu ba ne a siyasa, amma ya gargaɗi da kada a mayar da shi makami na tsoratarwa ko ware wasu.

“Ra’ayi ba laifi ba ne, amma kada ya zama hanyar tsoratarwa ko wariya,” inji shi.

Ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyar su tabbatar da cewa zaɓen fidda gwani ya gudana cikin gaskiya da adalci, tare da mutunta masu takara da wakilai.

“Dole ne tsarin ya kasance mai gaskiya domin har waɗanda suka yi rashin nasara su girmama shi,” ya ƙara da cewa.

Shettima ya roƙi waɗanda ka iya faɗuwa a zaɓen fidda gwani da kada su juya wa jam’iyyar baya ko rusa tsarinta saboda fushi.

“Siyasa tafiya ce mai tsawo. Ba a ƙone abin hawa saboda wata matsala a hanya,” inji shi.

Ya ƙara da cewa tarihin siyasar Nijeriya cike yake da misalan mutanen da suka faɗi a wani lokaci amma daga baya suka samu nasara mafi girma.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma jaddada cewa APC kada ta zama wanda za ta cutu da kanta sakamakon bambance-bambancen da ke cikinta, yana mai cewa wannan bambanci ƙarfi ne, amma dole a tafiyar da shi da adalci da ladabi.

Ya yabawa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa irin salon jagoranci da ya nuna na haɗa kai da juriya, yana mai cewa dimokuraɗiyya na bunƙasa ne ta hanyar sasanci da haɗin gwiwa.

A ƙarshe, Shettima ya yi kira ga shugabanni, masu neman takara, magoya baya da dukkan mambobin jam’iyyar da su kasance masu haƙuri, adalci da haɗin kai gabanin zaɓen 2027.

“Rufin wannan gida ya kare mu duka. Idan muka rusa shi saboda fushi, kowa zai fuskanci sakamakon,” inji shi.

By ukarofi