Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sallami Babban Daraktan Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur (NMDPRA), Malam Saidu Mohammed, ne a daidai lokacin da yake halartar wani muhimmin taro na ƙasa da ƙasa a ƙasar Jamus.
Rahotanni sun nuna cewa, Saidu Mohammed yana jagorantar tawagar NMDPRA da suka je birnin Berlin, domin halartar Taron Fasahar Bututun Mai (PTC), inda ma ya kasance yana gabatar da muƙala a lokacin da aka sanar da shi an cire shi daga muƙaminsa.
Wata majiya da ke tare da shi a Jamus ta bayyana cewa an isar masa da saƙon sallamar ne kai tsaye yayin da yake kan dandalin taron yana jawabi, lamarin da ya jawo mamaki a tsakanin mahalarta.
A baya, hukumar NMDPRA ta tabbatar da halartar shugaban nata a taron, inda ta wallafa a shafinta na X cewa Mohammed na jagorantar tawagar Nijeriya a taron da aka gudanar daga 27 zuwa 30 ga Afrilu, 2026 a Berlin.
Sai dai, kimanin awanni biyu bayan wannan sanarwa, mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya cire Mohammed daga muƙaminsa tare da naɗa Rabiu Abdullahi Umar a matsayin sabon shugaban hukumar.
Cire Mohammed ya zo ne bayan kusan watanni biyar kacal da karɓar muƙamin, bayan ya janye shirin shiga kwamitin gudanarwa na kamfanin Seplat Energy domin karɓar shugabancin NMDPRA.
Tun farko, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mohammed ne bayan murabus ɗin tsohon shugaban hukumar, Farouk Ahmed, a ranar 17 ga Disamba, 2025.
A cikin sanarwar, fadar shugaban ƙasa ta ce an ɗauki matakin ne domin amfanin jama’a, tare da jaddada ƙudurin gwamnati na tabbatar da ingantaccen shugabanci a muhimman hukumomi domin ƙarfafa tsaron makamashi, zurfafa gyare-gyaren ɓangaren mai, da kuma bunƙasa tattalin arziki mai ɗorewa.
Haka kuma, Shugaban ya gode wa Mohammed bisa gudunmawar da ya bayar yayin da yake riƙe da muƙamin, tare da masa fatan alheri a gaba.
Rahotanni sun kuma nuna cewa wannan ba shi ne karo na farko ba da Shugaba Tinubu ke sallamar wani babban jami’i yayin da yake kan aiki a ƙasashen waje ba, domin a watan Nuwamba 2025 ma ya cire Ogbonnaya Orji daga muƙaminsa na Babban Sakatare na NEITI yayin da shi ma yake wata tafiya ta aiki a ƙetare.
