Kaduna 2027: Bawa Garba na ƙara ɗaukar hankali da salon kusantar jama’a

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI, GOMBE

Yayin da siyasar zaɓen gwamnan Jihar Kaduna na 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, Hon. Usman Shehu Bawa Garba na daga cikin ‘yan siyasar da ke jan hankalin jama’a, musamman saboda salon shugabancinsa na kusantar al’umma da kuma haɗa kai.

A wata hira da manema labarai, masaniyar harkokin jama’a kuma ƙwararriya a fagen aikin jarida Gimbiya Abdu, ta bayyana Bawa Garba a matsayin shugaba da aka gina bisa kyawawan ɗabi’u na al’umma, taimakon jama’a da kuma sadaukar da kai wajen hidima.

Ta ce tarihin rayuwarsa da ayyukansa na ci gaba da jawo hankalin jama’a, ganin yadda yake fahimtar buƙatunsu da kuma ƙoƙarin magance su ta hanyoyi masu ma’ana.

An haifi Bawa Garba a watan Afrilu na shekarar 1973 a Kaduna, inda ya taso a gidan Alhaji Bawa Garba, fitaccen ɗan kasuwa da ya taka rawa wajen kawo talabijin ta tauraron dan adam a Arewacin Najeriya, tare da kafa kasuwar Baje Koli na ƙasa da ƙasa a Kaduna.

Wannan tarbiyya, a cewar Gimbiya Abdu, ta gina shi da jajircewa, hangen nesa da kuma jin nauyin al’umma.

Bawa Garba ya fara harkokin siyasa ne a jam’iyyar ANPP, daga bisani ya koma CPC, kafin ya zama ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Kaduna ta Arewa daga 2011 zuwa 2015, inda ya riƙe mukamin mataimakin shugaban kwamitin sadarwa.

A lokacin aikinsa, ya taka rawar gani wajen aiwatar da ayyuka a fannoni daban-daban da suka haɗa da ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwan sha da kuma ƙarfafa matasa, ciki har da kafa cibiyoyin ICT a makarantu domin inganta koyon fasahar zamani.

Har ila yau, ta hannun gidauniyarsa ta Shehu ABG, ya ci gaba da tallafawa ɗalibai ta hanyar bayar da guraben karatu, ɗaukar nauyin jarabawa da kuma horas da su kan harkokin ICT, musamman masu rubuta jarabawar JAMB.

Haka kuma yana tallafa wa cibiyoyin lafiya da ayyukan samar da ruwa.

Yanzu haka yana neman kujerar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, inda ya mayar da hankali kan tsaro, bunƙasa tattalin arziki da kuma ƙarfafa al’umma daga matakin ƙasa.

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin gogewarsa da kusancinsa da jama’a na sanya shi cikin jerin ‘yan takarar da ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa a zaɓen 2027.

By ukarofi