Hukumar IPAC ta Zamfara ta zaɓi sabbin shugabanni

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Hukumar majalisar bada shawara kan jam’iyyun siyasa, IPAC, ta zaɓi sabbin shugabannin ta a Jihar Zamfara, ba tare da hamayya ba don gudanar da harkokin hukumar na tsawon shekaru biyu masu zuwa.

An gudanar da zaɓen a jiya Juma’a, a hedikwatar hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta, INEC, da ke Gusau, wanda wakilan hukumar IPAC na ƙasa suka jagoranta, kuma jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, da hukumomin tsaro suka shaida.

Waɗanda aka zaɓa sun haɗa da Sulaiman Salisu na Jam’iyyar Action Peoples’ Party, APP, a matsayin Shugaba, Bashir Abdullahi Bungudu na Jam’iyyar Accord a matsayin Sakatare, da Paul Ezeanya na Action Alliance, AA, a matsayin ma’ajin kuɗi, da sauran jami’ai.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa an cike dukkan mukamai ba tare da Hamayya ba, bayan da jam’iyyun siyasa a jihar suka amince da yarjejeniyar.

Da yake jawabi ga sabbin shugabannin, shugaban IPAC na ƙasa, Dr. Yusuf Mamman Dantalle, ya bayyana zaɓen a matsayin na lumana, gaskiya, kuma abin koyi ga dimokuraɗiyya tsakanin jam’iyyu.

Dr. Dantalle, wanda Bashir Bala ya wakilta, ya yaba wa jam’iyyun Siyasa a Jihar ta Zamfara saboda ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu don gudanar da zaɓen Shugabannin hukumar IPAC cikin lumana.

Ya umarci sabbin shugabannin da su yi aiki a matsayin masu sulhu tsakanin jam’iyyun siyasa da kuma yin aiki kafaɗa da kafaɗa da INEC, hukumomin tsaro, da ƙungiyoyin farar hula kafin babban zaɓen 2027.

Da yake magana da manema labarai bayan kammala zaɓen, sabon shugaban na IPAC a Jihar ta Zamfara, Sulaiman Salisu, ya gode wa mambobin Jam’iyyun bisa amincewar da suka nuna masa ya zamo jagoran hukumar.

Ya yi alƙawarin gudanar da mulki mai adalci da haɗin kai.

“Ƙofofina a buɗe suke ga dukkan membobin IPAC.”

“Muna buƙatar haɗin kai don ƙarfafa tattaunawa tsakanin jam’iyyu da kuma tallafawa a tabbatar anyi zaɓe mai inganci a Jihar Zamfara a shekarar 2027,” in ji Salisu.

By ukarofi