Gwamnatin Katsina ta gina hanyoyi masu tsawon kilomita 200

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya ce gwamnatin sa ta gina hanyoyi masu tsawon kilomita 200 a faɗin jihar.

Gwamnan ya sanar da haka ne a lokacin ƙaddamar da hanyar Yanɗaki, Shinkafi zuwa Kofar Soro wanda gwamnan jihar Sokoto Alhaji Ahmed Aliyu ya ƙaddamar.

Dikko Raɗɗa ya yaba wa ɗan kwangilar da ya kammala aikin Kafin wa’adin da aka yi da shi.

Gwamnati ta kashe Naira biliyan 12.6

Haka kuma gwamnan Yobe Mai Mala buni ya buɗe tare da kaddamar da titin Shargalle zuwa Dutsi ta wuce Ingawa mai tsawon kilomita 39 da aka gina akan kuɗi Naira biliyan 13.9.

Buni ya yaba wa Gwamna Raɗɗa kan sabunta tsohon titin da ya shafe sama da shekaru 50 da ginawa.

Ya bayyana titin a matsayin muhimmin aiki da zai ƙara bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar a Ingawa, Gwamna Raɗɗa ya ce wannan aiki yana nuna ƙoƙarin gwamnatinsa wajen inganta ababen more rayuwa da ci gaban karkara.

Ya ce: “Wannan ba titin kawai ba ne, hanya ce mai muhimmanci da ke haɗa al’umma, tallafa wa noma da kasuwanci, kuma tana sauƙaƙa rayuwar jama’a.”inji Dikko.

Ya ƙara da cewa titin zai rage lokacin tafiya, ƙara tsaro, tare da buɗe sabbin damar kasuwanci ga mazauna Shargalle, Dutsi, Ingawa da sauran yankuna.

Gwamna Raɗɗa ya gode wa Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, bisa halartar taron a matsayin babban baƙo.

Ya kuma bayyana cewa titin yana da tarihi, domin an fara gina shi a zamanin marigayi Gwamna Balarabe Musa, sannan aka sake gyara shi a zamanin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’adua lokacin yana gwamnan Katsina.

Ya ce: “Yanzu mun sabunta titin domin ya dace da bukatun yau da na gaba.”

Gwamnan ya yabawa ma’aikatar ayyuka, gidaje da sufuri ƙarƙashin jagorancin Injiniya Sani Magaji Ingawa bisa kulawa da aikin yadda ya kamata.Haka kuma ya yabawa kamfanin Mothercat Limited da Al’Amin Consult bisa aiki mai inganci da suka yi.

Ya roƙi al’umma da su kula da titin domin ya ɗore.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kawo ayyukan alheri ga jama’a.

A wurin taron, Gwamna Buni ya karɓi mutane da dama da suka bar jam’iyyun adawa suka shiga jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan zai ƙara haɗin kai da zaman lafiya.

Kwamishinan Ayyuka, Injiniya Sani Magaji Ingawa, ya ce an kammala aikin cikin Naira biliyan 13.9, kuma kamfanin Mothercat Limited ne ya yi aikin tare da kulawar ma’aikatar da taimakon Al’Amin Consult.

Ya ce titin zai ƙara haɗin kai tsakanin Shargalle, Dutsi da Ingawa, ya bunƙasa noma da kasuwanci, ya rage lokacin tafiya, kuma ya ƙara tsaro.
Manajan Darakta na Mothercat Limited, Maroun Ghostine, ya ce an kammala aikin cikin watanni 12 maimakon watanni 16 da aka tsara, sakamakon haɗin kai da gwamnati.

Ya ce titin zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki, noma, lafiya da ilimi.
Taron ya samu halartar manyan jami’ai da suka haɗa da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Hon. Nasir Yahaya Daura; Ministan Gidaje, Injiniya Dr. Muttaqa Rabe Darma; tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika; da sauran manyan jami’ai da sarakuna.

By ukarofi