Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ƙungiyar Wamban Shinkafi Democratic Front a yayin taron ta na masu ruwa da tsaki a Gusau, ta ayyana sauya shekar Gwamna Dauda Lawal zuwa jam’iyyar All Progressives Congress APC a matsayin samar da sabuwar alƙiblar siyasar Jihar Zamfara kafin babban zaɓen 2027.
Taron, wanda aka gudanar a Taula Arena da ke babban birnin jihar, ya samu halartar shugabannin APC, ƙungiyoyin matasa da mata, dattawan al’umma, da abokan siyasa daga ƙananan hukumomi 14 na jihar.
A jawabin da ya yi wa taron, jagoran ƙungiyar kuma tsohon ɗan takarar gwamna a Jam’iyyar APGA, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya ce manufar taron ita ce, su nuna a hukumance yin maraba da Gwamna Dauda Lawal cikin jam’iyyar APC.
“Taronmu na yau abin tarihi ne. Mun zo nan ne don maraba da Mai Girma Gwamna Dauda Lawal, cikin APC. Wannan shi muka kira sabon sauyi a Jihar Zamfara kafin 2027,” in ji Shinkafi.
Ya ƙara da cewar ƙungiyar sa da magoya bayan sa sun aminta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sake tsayawa takara a karo na biyu don inganta rayuwar alummar Nijeriya a zaɓen 2027 da ke tafe.
“Ƙungiyar Wamban Shinkafi Democratic Front tana mai bayyana wa duniya cewar taron mu na yau ya aminta da tsayawar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu takara a karo na biyu don samun damar kammala muhimman ayyukan cigaban alummar Nijeriya baki ɗaya.” A cewar Shinkafi.
Shinkafi ya ambaci haɗin kai da kishin ƙasa a matsayin ginshiƙin nasarar APC a Zamfara, yana mai kira ga tsoffin mambobi da sabbin mambobi da su kusanci juna.
“Ficewar Gwamna Dauda Lawal zuwa APC shaida ce ta nasarar APC a jihar kuma hakan yana nuna cewa APC ita ce jam’iyyar da za tayi nasara a 2027 da ikon Allah,” in ji shi.
Ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su guji maganganun raba kan jama’a su yi aiki a matsayin iyali ɗaya.
“Dole ne mu ci gaba da kasancewa tare don nasarar jam’iyyar da kuma ci gaban jihar, kuma kada muradun mutum ɗaya su wuce muradun gama gari.”
Shinkafi ya yaba da aikin Gwamna Lawal tun lokacin da ya hau mulki, yana mai bayyana manufar gwamnatinsa a matsayin aikin ceto wanda ya kawo canji a Zamfara.
“Gwamna Dauda ya taɓa kowane fanni na tattalin arziki, tun daga ilimi, lafiya, noma, tsaro, ma’aikatan gwamnati, hanyoyin sadarwa, albarkatun ruwa, ƙarfafa matasa da sauransu,” in ji shi.
Ya lissafa ci gaba da sabunta birane a Gusau, biyan kuɗin tallafi, ɗaukar ma’aikatan lafiya, da shirye-shiryen tallafawa noma a matsayin shaidar Zamfara ta komo Jihar ta zamani a ƙarƙashin mulkin Gwamna Dauda Lawal.
Shinkafi ya yi kira ga magoya baya da su yi gangami don sake tsayawa takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma sake tsayawa takarar Gwamna Lawal a wa’adi na biyu a 2027.
“Ina kira ga dukkan magoya bayanmu da su goyi bayan takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 da Gwamna Dauda Lawal don bai wa gwamnati damar samar da ƙarin riba ga dimokuraɗiyya a Jihar Zamfara,” in ji Shinkafi.
Hakazalika ya jaddada cewa haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya zai jawo ƙarin ayyuka da inganta tsaro a jihar.
