NUJ a Katsina ta jaddada ƙudirinta na ƙarfafa da kare haƙƙin ‘yan jarida a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar yan jarida ta ƙasa reshen jihar Katsina ta jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa kare yancin yan jirada wanda ginshiƙi ne na ɗorewar demokradiyya.

A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun shugaba da sakataren ƙungiyar a Katsina Aminu Garba Danɗagoro da Abbas Bamalli, ƙungiyar ta nuna damuwa kan yadda a ke cin zarafi da katsalandan ga aikin jarida.

Ƙungiyar itama ta bi takwarorinta wajan bikin ranar yancin ‘yan jarida ta duniya.

Ƙungiyar ta ce wannan matsala ga yancin ‘yan jarida kamar yadda tsarin mulkin ƙasa kuma na iya kawo rauni ga dimokuraɗiyya.

“Ya zama wajibi a bar manema labarai su gudanar da aikin su ba tare da cin zarafi ba,”Inji NUJ Katsina.

NUJ ta kuma buƙace jami’an gwamnati da na tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su mutunta da kare haƙƙin ‘yan jarida a ko da yaushe.

Ta buƙaci manema labarai da a ko da yaushe suna tantance da tabbatar da sahihancin labari domin zaman lafiya, haɗin kan ƙasa.

Ƙungiyar ta nuna goyon bayan ta ga ƙoƙarin da manema labarai da gidajen jaridu a ƙoƙarin da suke na ilmantar da faɗakar da al’umma.

By ukarofi