Al’ummar Wase sun nemi Ahmed Idris Wase ya sake takarar Majalisar Tarayya a karo na 6

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU, Jos

Al’ummar mazaɓar kujerar ɗan Majalisar Tarayya ta Wase a Jihar Filato da magoya bayan Jam’iyyar APC ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna Wase Equity Projects, sun haɗa kuɗi har Naira Miliyan 10 domin saya wa tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, kuma ɗan majalisa mai wakiltar Wase, Ahmed Idris Wase, takardar neman tsayawa takara, domin ya cigaba da wakiltar yankinsu a Majalisar Ƙasa.

Dubban jama’a ne maza da mata suka yi cincirindo don tarbar ɗan majalisar da tawagarsa, yayin da ya shiga garin Wase, domin amsa kiran jama’ar mazaɓarsa da suka neme shi saboda su miƙa masa shaidar tsayawa takarar da suka saya masa.

Da yake ganawa da manema labarai, ɗan Majalisar Dokoki ta Jihar Filato, Ibrahim Galadima ya bayyana cewa, babu shakka Ahmed Idris Wase ya taka rawar gani, bisa irin ɗimbin ayyukan da yake gudanarwa, wanda ya zarce na wani Gwamnan.

Ya ce, Maje, kamar yadda aka saba kiransa a gida, ya yi sanadin kafa wasu dokoki masu muhimmanci da suka haifar da ayyukan alheri da dama da jama’ar mazaɓar Wase suka amfana da su, tun daga hanyoyi, zuwa ɓangaren lafiya, harkar ilimi, harkar tsaro da samar da ayyukan yi ga daruruwan matasa, a ciki da wajen Wase.

A saƙonsa na godiya ga jama’ar Wase, bisa irin goyon baya da soyayya da suka nuna masa, tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar, ya ba da tabbacin cewa, ba zai taɓa ba su kunya ba, kuma zai cigaba da jawo manyan ayyukan gwamnatin tarayya zuwa yankin.

Kafin wannan taro dai, wasu gungun ýan siyasa a garin na Wase sun gudanar da wani gangami na kira da a riƙa amfani da tsarin karɓa-karɓa a tsakanin ƴan siyasar da,suka fito daga ɓangarorin mazaɓar, domin bai wa kowa damar neman wakilcin wannan kujera.

Sai dai a cewar shugabannin Wase Equity Project, wannan shawara ta su ta saɓawa tsarin mulkin ƙasa, da tsarin jam’iyyar APC, don haka matuƙar Ahmed Idris Wase zai cigaba da nuna kyakkyawan wakilci a majalisa to, babu za su taɓa gajiyawa da zaɓarsa ba.

By ukarofi