Daga USMAN KAROFI
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, sun kai ziyara hedikwatar jam’iyyar Nigerian Democratic Congress (NDC) da ke Abuja a ranar Lahadi. Haka kuma, Sanata Victor Umeh ya halarci taron, abin da ya ƙara jawo hasashen cewa suna shirin shiga jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa wannan ziyara ta zo ne bayan Peter Obi ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), inda ya danganta hakan da rikice-rikicen cikin gida da rashin jituwa a shugabanci. A ‘yan watannin nan, ana alakanta shi da yunƙurin kafa wata babbar haɗakar jam’iyyun adawa domin ƙalubalantar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
A nasa ɓangaren, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ke jagorantar tafiyar Kwankwasiyya, bai sanar da ficewarsa daga ADC a hukumance ba, amma masu sa ido kan siyasa na ganin ziyararsa hedikwatar NDC na iya nuna sauyin siyasa mai zuwa. Ana kuma kallon yiwuwar hadin gwiwar “OK” a matsayin wata hanya da za ta iya samar da tikitin takarar shugaban ƙasa mai ƙarfi a zaɓen 2027.
