
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), ta ƙaddamar da jigilar Hajjin 2026 da jirgin farko daga Abuja, inda aka ɗauki maniyyata 474 daga Jihar Kogi zuwa ƙasar Saudiyya.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a Abuja bayan sauya shirin farko da aka yi na tashi daga Jihar Ogun.
Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen tafiyar da harkokin hukumar bisa tsari.
Ya kuma buƙaci maniyyata da su bi dukkan ƙa’idoji musamman amfani da katin Nusuk, tare da tabbatar da cewa an kammala dukkan shirye-shirye ciki har da masauki a Mina.
Haka kuma, ya gargaɗe su da su ƙaurace wa dukkan wata hanya ta saɓa wa sharuɗɗa ko dokokin da aka gindaya, yana mai cewa Saudiyya ta tanadi matakai masu tsauri akan waɗanda aka samu da hannu a aikata ire-iren laifukan.
Da yake jawabi, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya roƙi maniyyatan da su zama jakadu nagari na Nijeriya, yayin da sauran jami’ai suka buƙaci su kasance masu ladabi, gaskiya da kuma yi wa ƙasa addu’ar zaman lafiya.
