
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon gwamnan Jihar Anambara, Peter Obi kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyya LP a zaɓen 2023 da tsohon gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, sun shiga jam’iyyar NDC, wato National Democratic Congress NDC a hukumance.
Manyan ‘yan siyasar biyu sun kammala ɗaukar wannan mataki ne a ranar Lahadi bayan ganawa da jagoran jam’iyyar kuma tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson a Abuja, inda suka sanar da sauyin tafiyarsu zuwa sabuwar jam’iyyar adawa yayin tunkarar babban zaɓen 2027.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da ganin sauye-sauyen harkar siyasar Nijeriya, musamman yayin da jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin haɗa kai domin tunkarar zaɓen.
A yanzu dai hankalin al’umma ya koma kan yadda wannan haɗaka za ta sauya fasalin siyasar Nijeriya gaba ɗaya musamman ganin yadda ‘yan siyasar biyu ke da ƙarfi a sassa da dama ƙasar.
