Wanda ya kafa CNN, Ted Turner, ya rasu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ted Turner, fitaccen ɗan kasuwa kuma wanda ya kafa shahararriyar kafar yaɗa labarai ta CNN, ya rasu yana da shekaru 87 a duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa Turner, wanda ya yi suna a harkokin kasuwanci, wasanni da kafafen yaɗa labarai, ya rasu ne ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026.

Kamfanin Turner Enterprises ya tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da ya fitar, sai dai bai bayyana musabbabin mutuwar ba.

Tun a watan Satumban 2018 ne Turner ya bayyana cewa yana fama da cutar Lewy body dementia, wata cuta mai lalata jijiyoyin ƙwaƙwalwa da ke shafar ƙwaƙwalwa da motsin jiki.

Ted Turner ya fara gina daularsa ta kasuwanci ne bayan ya karɓi ragamar kamfanin tallace-tallacen alluna na mahaifinsa, kafin daga bisani ya sayi tashar talabijin a shekarun 1970, matakin da ya zama tushen kafa babbar daular kafafen yaɗa labarai.

Daga baya ya kafa CNN, tashar talabijin ta farko da ke watsa labarai na awanni 24 a duniya, lamarin da ya sauya salon yada labarai gaba ɗaya tare da ɗaga martabarsa zuwa cikin manyan masu tasiri a kafafen yaɗa labarai da nishaɗi a Amurka.

Kamfanonin Turner sun shahara wajen watsa labarai, wasanni, tsoffin fina-finai da shirye-shiryen nishaɗi, abin da ya ƙara bunƙasa daularsa.

Ya kuma mallaki kamfanin shirya fina-finai na MGM/UA kafin daga bisani ya haɗa kamfaninsa na Turner Broadcasting System da Time Warner a shekarar 1996, a wata babbar yarjejeniyar kasuwanci da ta girgiza duniyar kafafen yaɗa labarai.

Bayan haɗewar kamfanonin, Turner ya jagoranci ɓangaren tashoshin cable na sabon kamfanin kuma ya kasance babban mai hannun jari, duk da cewa daga baya ya fuskanci ƙalubale wajen daidaitawa da tsarin gudanarwa na manyan kamfanoni, lamarin da ya sa ya rasa cikakken iko kan cibiyoyinsa.

Baya ga harkokin yaɗa labarai, Turner ya yi suna wajen manyan yarjejeniyoyin kasuwanci, mallakar ƙungiyoyin wasanni, da kuma aurensa da fitacciyar jarumar Hollywood Jane Fonda.

Haka kuma ya kasance jagoran tawagar tseren jiragen ruwa tare da bayar da gudunmawa sosai wajen ayyukan jinƙai da kare muhalli.

An haifi Robert Edward “Ted” Turner III a birnin Cincinnati na jihar Ohio a watan Nuwamban 1938. Ya yi karatu a makarantar soja ta kwana a Tennessee sannan ya halarci Jami’ar Brown, sai dai an kore shi kafin ya kammala karatunsa.

Turner ya karɓi ragamar kasuwancin iyalinsu ne bayan mahaifinsa ya kashe kansa sakamakon matsalolin kuɗi da suka addabi kamfanin.

Rasuwarsa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tuna rawar da ya taka wajen sauya fasalin aikin jarida da kafafen yaɗa labarai a duniya.

By ukarofi