Daga AISHA ASAS
*Uwargidan shugaban ƙasa ta zargi kalaman da haddasa ƙiyayya da tashin hankali
*Trump ya nemi a kori mai gabatar da shirin, yayin da shiru ya mamaye ABC
Wata sabuwar taƙaddama mai ɗaukar hankali ta ɓarke a Amurka bayan Uwargidan Shugaban ƙasa, Melania Trump, ta fito fili tana kakkausar suka ga fitaccen mai gabatar da shirin dare, Jimmy Kimmel, inda ta buƙaci tashar ABC ta ɗauki matakin ladabtarwa a kansa, har ma da yiwuwar korarsa.
Wannan martani mai zafi ya biyo bayan wasu kalamai na barkwanci da Kimmel ya yi a cikin shirinsa na “Jimmy Kimmel Live”, inda ya yi kwaikwayon jawaban da ake yi a taron shekara-shekara na ‘yan jarida da ake kira White House Correspondents’ Dinner, taro da aka saba amfani da shi wajen yin barkwanci kan shugabanni da fitattun mutane.
A cikin shirin nasa, Kimmel ya yi tsokaci kan shugaban ƙasa Donald Trump da matarsa, inda ya furta kalamai da suka jawo cece-kuce, ciki har da bayyana Melania da cewa tana da “kyalli irin na mace da take jiran ta zama bazawara” kalma da ta fusata magoya bayan gwamnatin Trump.
Ba a nan ya tsaya ba, domin ya kuma nuna wani bidiyo na bogi wanda aka kirkira ta hanyar fasahar zamani, inda aka nuna kamar Melania da ɗanta Barron suna zaune a cikin dakin studio suna sauraron shirin, abin da Trump ya musanta yana mai cewa hakan bai taɓa faruwa ba kuma ba zai faru ba.
Rikicin ya ƙara ɗaukar sabon salo ne bayan da Trump ya danganta kalaman Kimmel da wani mummunan lamari da ya faru washegari, inda wani da ake zargi ya yi yunƙurin shiga wajen taron White House Correspondents Dinner ɗauke da makamai masu haɗari kamar bindigogi da wuƙaƙe.
Trump ya bayyana cewa, wannan mutumin ya zo da wata “manufa mai hatsari”, yana mai nuni da cewa irin kalaman Kimmel na iya ƙarfafa tashin hankali.
A cikin sakon da ta wallafa a kafafen sada zumunta, Melania Trump ta bayyana cewa, kalaman Kimmel sun wuce iyakar barkwanci, tana mai cewa: “Kalaman ƙiyayya da tashin hankali da Kimmel ke yi na nufin raba kan ƙasarmu. Wannan ba barkwanci ba ne, kalamai ne masu lalata da ƙara tsananta rashin lafiya ta siyasa a Amurka.”
Ta ƙara da cewa bai kamata a bar irin waɗannan mutane su rika shiga gidajen jama’a kowace rana ta hanyar talabijin suna yaɗa saƙon ƙiyayya ba.
Melania ta kuma zargi Kimmel da ɓoyewa a bayan kariyar da tashar ABC ke ba shi, tana mai cewa, lokaci ya yi da tashar za ta ɗauki mataki.
A nasa ɓangaren, Donald Trump ya ƙarfafa wannan kira, inda ya bayyana Kimmel a matsayin wanda bai iya barkwanci ba, kuma yana amfani da kafar talabijin wajen yaɗa abubuwan da suka wuce gona da iri.
Ya buƙaci kamfanin Walt Disney wanda ke mallakar ABC da ya ɗauki matakin gaggawa na korar Kimmel.
Abin lura shi ne, a wannan shekarar ba a gudanar da barkwancin gargajiya a taron White House Correspondents’ Dinner ba kamar yadda aka saba, domin an shirya cewa wani mai sihiri ne zai jagoranci taron maimakon ɗan barkwanci.
Haka kuma taron ya ƙare da wuri bayan wani hari da aka kai a wurin taron da ke otal ɗin Washington Hilton, abin da ya ƙara dagula yanayin tsaro da tashin hankali a lokacin.
Saboda haka, Kimmel ya ce ya ɗauki nauyin yin irin barkwancin da aka saba yi a taron a cikin shirinsa, yana mai cewa shugaban ƙasa bai son irin wannan barkwanci.
A cikin shirin nasa, Kimmel bai tsaya kan shugaban ƙasa kaɗai ba, har ma ya yi tsokaci kan wata takarda da aka shirya game da Melania a kamfanin Amazon, yana mai cewa wannan shi ne “fim ɗin farko a duniya da ba shi da motsi.”
Haka kuma ya soki Trump kan wasu batutuwa da suka haɗa da alaƙarsa da wasu fitattun mutane da kuma hoton da aka kirkira ta hanyar AI da ya nuna shi kamar wani mutum mai tsarki.
Duk da wannan hayaniya, har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, babu wata amsa kai tsaye daga Jimmy Kimmel ko tashar ABC dangane da zarge-zargen da ake yi musu.
Sai dai a baya, tashar ta taɓa dakatar da shirin Kimmel na ɗan lokaci sakamakon wasu kalamansa da suka jawo cece-kuce, lamarin da ke nuna cewa wannan ba shi ne karo na farko da yake shiga irin wannan rikici ba.
Yayin da wannan rikici ke ƙara ɗaukar hankali a kafafen yaɗa labarai, tambayar da ke gaban jama’a ita ce: shin barkwanci yana da iyaka idan ya shafi shugabanni da iyalansu? Ko kuwa irin wannan matsin lamba na iya zama barazana ga ‘yancin faɗar albarkacin baki a kafafen watsa labarai?
