Sojoji sun kama mutane shida da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sojoji na rundunar 17 Brigade da haɗin gwiwa na jami’an hukumar NDLEA sun kama mutane shida ɗauke da miyagun ƙwayoyi a wani samame da suka kai a ƙauyen Dawo a ƙaramar hukumar Malumfashi bayan samun bayanai na sirri.

Majiya daga hukumar tsaron ya ce a yayin gudanar da samamen, jami’an tsaron sun sami garin tabar wiwi mai nauyin kilogram 82.5 a maɓoyar dillalan ƙwayoyin.

Akwai kuma kilogiram 15.7 na Extol 5.1 da kilogiram 8 na D5 duk a maɓoyar ta su.

A cewar rundunar sojojin,da zarar sun kammala bincike za su miƙa waɗanda ake zargi ga hukumar hana sha da fatauci na miyagun ƙwayoyi NDLEA a Katsina.

Wannan samame da jami’an tsaron suka kai na daga cikin ƙoƙarin da suke yi na daƙile sha da fataucin miyagun kwayoyi da sauran ayyukan ɓata gari a faɗin jihar.

Yanzu haka dai haɗin gwiwa na jami’an tsaro da suka haɗa da yan sanda, jami’an NDLEA,yan hisbah da yan banga na nan na sintiri a unguwar Unwala cikin birnin Katsina domin tabbatar da zaman lafiya bayan da unguwar ta yi ta fama da faɗace faɗacen ƙauraye.

By ukarofi