Sace ɗaliban NSUK: ‘Yan sanda sun kama mutum biyu

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafia

Hedikwatar ‘yan sanda ta Jihar Nasarawa ta sanar wa jama’a samun wani babban nasara a binciken da ta ke gudanarwa a kan sace ɗaliban fannin karatun Injiniya na babbar jami’ar jihar da ke Gudi inda a yanzu haka tace ta cafke mutum biyu cikin waɗanda ake zargi da aikata ɗanyen aikin tare da ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.

Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan ne jaridar Manhaja ta ruwaito labarin wasu miyagun mutane ‘yan bindiga waɗanda suka kai hari fannin karatun Injiniya da ke garin Gudi a ƙaramar hukumar Akwanga inda suka yi awon gaba da kimanin ɗalibai shida.

Daga bisani dai bisa ayyukan bincike da tattara bayanan sirri da kuma aikin dabara na musamman da jami’an ‘yan sandan suka fara gudanarwa nan take jim kaɗan da aukuwar mummunar lamarin a yanzu haka rundunar ‘yan sandan jihar tayi nasara inda tace ta kama mutum biyu da ake zargi da alaƙa da satar.

Waɗanda ake zargin a cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Rahman Nansel sune Abdullahi Yeyi Haro wanda ake zargin shi ne shugaban ƙungiyar masu garkuwa da mutanen da kuma Basiru Abdullahi.

A cewar SP Rahman Nansel an kama su ne bayan bincike mai zurfi da ayyuka na dabara da aka yi domin wargaza ƙungiyar masu laifi da ke da hannu a satar.

Hedkwatar ‘yan sanda ta kuma sanar da cewa tana farin cikin sake sanar da cewa an sako ɗaliban da aka sace cikin ƙoshin lafiya kuma an mayar da su ga iyalansu kuma halin yanzu waɗanda abin ya shafa suna karɓar kulawar likita da sauran tallafi bayan abin da suka fuskanta.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Nasarawa, CP Shetima Jauro Mohammed psc, mnips, ta bakin SP Rahman Nansel ya yabawa jami’an da suka shiga aikin bisa ƙwarewarsu da juriya da jajircewarsu wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al’umma a faɗin jihar.

Ya sake jaddada ƙudurin hedikwatar na kawar da kowane irin laifi a jihar Nasarawa musamman garkuwa da mutane da sauran laifuka masu tsanani da tashin hankali.

Kwamishinan ‘yan sanda ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar na cigaba da gudanar da cikakken bincike domin kama sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere da kuma gurfanar da duk waɗanda ke da hannu a laifin a gaban shari’a.

Har ila yau hedikwatar ta yaba wa jama’a bisa goyon baya da hadin kai inda bayanan da suka bayar cikin gaggawa suka taimaka sosai wajen samun wannan nasara.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Nasarawa Mohammed Shatima Jauro daga ƙarshe sai ya sake yin amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga ‘yan ƙasa gaba ɗaya da su cigaba da kasancewa a faɗake tare da bai wa hukumomin tsaro bayanai masu amfani domin hana laifi kafin faruwa da kuma amsa kiran gaggawa, inda ya ƙara da cewa hedikwatar ‘yan sanda ta jihar Nasarawa ta dage kan kare rayuka da dukiyoyin al’umma kuma tana tabbatar da cewa masu laifi ba za su sami wurin ɓoyewa a cikin jihar ba.

By ukarofi