Da Ɗumi-ɗumi: An kammala zaɓen majalisar wakilai a wasu sassan Akwanga na jihar Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafia

A halin yanzu an kammala wasu daga cikin zaɓukan fitar da gwani na ‘yan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressive Congress (APC) daga Arewacin jihar Nasararsa inda a yanzu ake cigaba da tattara ƙuri’un a VIP lodge dake nan cikin garin Akwanga hedikwatar karamar hukumar Akwanga a jihar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an kaɗa ƙuri’un ne cikin kwanciyar hankali cikin tsarin ƙato bayan ƙato kamar dai yadda hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta tanadar.

Wasu manyan masu faɗa aji a ƙaramar hukumar ta Akwanga ciki har da shugaban ƙaramar hukumar Safiyanu Andaha wanda har iya yau shine shugaban ƙungiyar duka shugabannin ƙananan hukumomin jihar sun bayyana gamsuwarsu da tsari da Kuma yanayin kaɗa ƙuri’un inda suka kuma yaba wa masu kaɗa ƙuri’un wato mambobin jam’iyyar APC mai ci a jihar ɗin dangane da abinda suka bayyana a matsayin halin dattaku da suka nuna da kuma cikakken haɗin kai da biyayya da suka nuna wa jami’an zaɓen kafin lokaci da kuma bayan kaɗa ƙuri’un inda suka buƙace su su cigaba da hakan.

By ukarofi