‘Bisa kure aka yanken hukunci’, bayan shekaru a kurkuku, ɗan Boko Haram, Kabiru Sakkwato na neman a soke hukuncin ɗaurin rai-da-rai akansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen ɗan ta’addar nan da ake zartarwa wa hukunci, Kabiru Umar da aka fi sani da Kabiru Sakkwato, ya ce an yi kuskuren yanke masa hukunci ne akan hannu a ta’addanci a shekarar 2013, inda a yanzu ya buƙaci Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta ƙalubalanci hukuncin ɗaurin rai-da-rai akansa.

Sababbin takardun ktou da jaridar NewsPointNigeria ta samo sun nuna cewa Umar, ta lauyoyinsa Don Akaegbu da Kamfani, sun shigar da ƙara mai ɗauki kwanan wata 13 ga watan Mayu, 2026 ta neman ƙara tsawon lokacin ɗaukaka ƙara akan hukuncin da Mai Shari’a A.F.A. Ademola na Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ya yi a ranar 20 ga watan Disambar 2013.

Ƙorafin na neman kotun da ta ƙyale shi ya yi amfani da damar da dokar ƙasa ta ba shi na ɗaukaka ƙara akan lokaci kamar yadda sashe na 6(6)(b) da na 36 na dokar ƙasa gyaran 1999 suka tanada.

An yanke wa Umar hukunci ne akan laifuka biyu na zargin kitsa ayyuka ‘yan ta’adda da rashin bayar da bayanai akan al’amuran ta’addanci.

A takardar da aka gabatar da ƙarar, mai shigar da ita ya ce an samu jinkirin haka ne sakamakon ƙalubalen da suka fi ƙarfin ikonsa ciki har da tsawaita tsarewa da sauya gidajen gyaran hali da kuma mutuwar lauyoyi biyu da aka ware domin su gabatar da ƙarar da aka ɗaukaka a kotu.

Wani Lawal Suleiman, wanda ɗa ne ga Umar Sakkwato ya ce bayan tsawon lokaci sun gano cewa yana tsare ne a kurkukun Kirkiri da ke jihar Legas a watan Maris, 2026.

Ya bayyana cewa, sauye-sauyen gidajen gyaran hali ga Umar ya sanya ‘yan uwansa a Sakkwato ba sa iya samun damar ganawa da shi da kuma ƙara matsi ga halin yau da kullum ga iyalansa.

Kazalika, ya ce Umar na cikin mawuyacin halin lafiya a zamansa na tsawon shekaru a kurkuku sakamakon rashin samun kulawa.

By Babaji