
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta dakatar da taurarin fim guda biyu, wato Amina Uba da aka fi sani da Amina Rani da kuma Adam Garba da aka sani da Raba Gardama, bisa zargin su da fitar da bidiyon baɗala acikin al’umma.
A cewar Babban Sakataren hukumar, Abba El-Mustapha, an dakatar da taurarin biyu ne na tsawon shekara guda daga shiga dukkan harkokin fim a Jihar Kano bisa saɓa wa dokokin hukumar.
A wata sanarwa da Kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a ranar Lahadi, an yi gargaɗin cewa matuƙar aka saɓa wa hukuncin, akwai matakin zuwa kotu akan haka ga dukkan wanda ya shafa.
Sanarwar ta kuma yi kira ga daraktoci da furodusoshi a masana’antar finafinan da su tabbatar da yin biyayya ga matakin, tana mai cewa za a hukunta dukkan wanda ya saɓa wa hakan kamar yadda doka ta tanada.
Kazalika, ta ce zargin aikata baɗala a bidiyon ya haddasa fargaba a sassan jihar, inda ta ce hukumar tana da sahalewar doka na ta dakatar da kowane jarumi ko jaruma da aka samu da taka dokar hukumar.
Har ila yau, sanarwar ta gargaɗi masu ruwa da tsaki na masana’antar Kannywood da su kiyaye dukkan wani aiki da ka iya ɓata musu suna da daraja a idon al’umma.
