Ɗan Majalisar Wakilai, Yusuf Gagdi ya faɗi a zaɓen fidda gwanin APC a Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Pankshin/Kanke/Kanam, Yusuf Gagdi ya faɗi a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a Jihar Filato.

An sanar da sakamakon zaɓen ne a Ƙaramar Hukumar Pankshin daga Baturen zaɓen yankin, Daspan Ishaya, wanda ya ayyana Dakta John Tongshinen a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun kuri’u 29,968.

Gagdi, wanda ke neman koma wa kujerar a karo na biyu, ya samu ƙuri’a 5,849 yayin da wani takara mai suna John Pia, ya samu guda 51.

Dalla-dallar bayanan sakamakon zaɓen ya nuna cewa Tingshinen shi ne wanda ya yi nasara a dukkan ƙananan hukumomi ukun mazaɓar.

A Pankshin Tongshinen ya samu ƙuri’a 13,155 yayin da Gagdi ya samu 1,072. A Kanke kuwa, Tongshinen ya samu guda 6,438 yayin da Gagdi ya samu 126.

Haka ma a Kanam, Tongshinen ya yi nasara da guda 10,375, sai Gagdi mai guda 4,651.

Da yake sanar da sakamakon, Ishaya ya ce an samu sakamakon ne daga yankunan mazaɓu da dama na ƙananan hukumomin, inda ya ce aikinsa shi ne sanar da jimillar sakamakon zaɓen da aka tattara.

By Babaji