Sarkin Malaman Gaya, Sheikh Munzil ya cika shekara biyu a sarauta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin, 17 ga watan Mayu, 2026 ne Sheikh Munzil ya cika shekara biyu cif a Sarautar Sarkin Malaman Gaya bayan gadar mahaifinsa a muƙamin.

A wata takarda da ya fitar, Sheikh Munzil ya godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa ƙaddara masa samin damar da ya samu, yana mai addu’ar fatan samun rahama ga marigayin mahaifin nasa da ya bar muƙamin.

Ya kuma yi godiya ga Mai Martaba Sarkin Gaya, Kirmau Mai Gabas, bisa amincewa da ya yi da shi waje naɗa shi ia matsayin.

Haka kuma, ya miƙa godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf bisa zama hakimi na farko da ya sanya wa hannu domin tabbatar da shi a matsayin daga hawansa a 2023.

Sarkin malaman ya ce, acikin shekaru biyun, ya sami damar samar da ayyuka masu ɗimbin amfani ga Masarautar Gaya da al’umma baki daya.

“Ga kadan daga cikin abubuwan da aka samu:

  1. Gina da Samar da Masallatan Juma’a
    Mun samar da masallatan Juma’a dayawa domin karfafa addini da saukaka ibada ga al’umma.
  2. Samar da Rijiyoyin Borehole
    Mun samar da rijiyoyin burtsatse domin rage matsalar ruwa a wasu yankuna na Masarautar Gaya.
  3. Tallafin Abinci da Azumi
    Mun gudanar da rabon tallafin danyen abinci ga mata marasa karfi na sama da mata 1000 wanda aka basu Shinkafa da Mai hade da dabino.
  4. Ciyar da Mutane Sama da 3,000 a Ramadan tare da bawa kowanne mutum lemon bawo da pure tun daga 2 ga watan Ramadan har karshen Ramadan, kuma muka cigaba dayi bayan Sallah
    An samar da dafaffen abinci da ake ciyarwa a gidan Sarki, wanda sama da mutane dubu uku ke amfana da shi.
  5. Horar da Limamai tare da Hadin Gwiwar Malaman Al-Azhar
    Malamai daga jami’ar Al-Azhar ta kasar Masar sun zo Gaya inda suka gudanar da bitar kwanaki uku ga limamanmu.
  6. Tura Limamai 10 zuwa Kasar Masar
    Daga cikin limaman da aka horas, an zabi guda 10 domin tafiya kasar Masar na tsawon wata shida domin kara kwarewa a harkar limanci.
  7. Samar da Ayyukan Yi
    Mun taimaka wajen samar da ayyukan yi da hanyoyin dogaro da kai ga matasa.
  8. Tura Dalibai 10 zuwa Almajiri Commission
    Mun samu damar kai yara 10 daga Masarautar Gaya zuwa makarantar Almajiri Commission, inda suka yi karatu na tsawon wata 11 karkashin tallafin gwamnatin tarayya, tare da damar fita kasashen waje domin kara ilimi.
  9. Shirye-shiryen Layya ga Dubban Jama’a
    A bana mun samar da dimbin kayan layya da za a rabawa sama da mutane 5,000 a fadin Masarautar Gaya. Hadin Kan Malamai da Zaman Lafiya.
    A karkashin jagorancinmu, babu wata matsala ta addini a Masarautar Gaya”, kamar yadda ya bayyana.

Ya ƙara da cewa: “Mun kafa Majalisar Ƙoli ta Malaman Masarautar Gaya, wacce ta haɗa malamai daga Tijjaniyya, Ƙadiriyya da Izala, kuma dukkansu suna aiki tare cikin haɗin kai da fahimtar juna.”

A cewarsa, waɗannan kaɗan ne daga cikin ayyukan da aka samu acikin ƙasa da shekaru biyu na jagorancinsa, yana mai addu’ar Allah Ya ƙara musu ikon yi wa addini da al’umma hidima cikin gaskiya, adalci.

By Babaji