Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta bada belin El-Rufa’i akan miliyan N100

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i akan Naira miliyan 100 da gabatar da mutum ɗaya da zai tsaya masa.

Alƙalin a yayin hukuncin a yau Litinin, ta ce wajibi ne wanda zai tsaya masan ya zama yana zama a unguwar Maitama ko gundumar Asokoro na birnin tarayya Abuja, kuma sai ya bayar da takardar mallakar fili ta asali ga ofishin rajistar kotun.

Haka kuma, wajibi ne sai ya zama ma’aikacin gwamnati wanda bai yi ƙasa da muƙamin mai matsayi na 17 ba, sannan ya miƙa shaidar karɓar albashin aƙalla watanni uku.

Mai Shari’ar ta kuma umarci mai tsayawar da ya gabatar da miƙa takardar amsa ƙorafi, shiga lamarin bada beli da kuma miƙa hoton fuska (fasfo) ga ofishin rajistar.

Kazalika, shi ma El-Rufa’in sai ya miƙa baki ɗaya fasfonsa na ƙasa-da-ƙasa ga kotun bayan umarnin miƙa takardar tantancewa daga ɓangaren mai tsayawar ya tabbata tare da shaidar biyan haraji na tsawon watanni shida.

Har ila yau, kotun ta umarci tsohon gwamnan Kadunan da ya riƙa zuwa ofishin hukumar tsaro ta farin kaya DSS, a ranar Juma’ar ƙarshe ta kowane wata da misalin ƙarfe 10 na safe yana sanya hannun halarta har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.

Ta kuma yi gargaɗin cewa matuƙar aka ƙi biyayya ga umarnin, hakan ka iya sa a soke bayar da belin.

Kotun ta kuma umarci El-Rufa’i da ya samo wasiƙar amincewa daga Shugaban Majalisar Sarakunan Kaduna tare da miƙa mata.

By Babaji