Wawaye ne kaɗai ke tunanin ina yi wa Tinubu aiki, inji Kwankwaso

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi watsi da zarge-zargen da ke cewa yana yi wa Shugaba Bola Tinubu aiki a ɓoye don a sake zaɓar sa a zaɓen 2027, yana mai bayyana masu iƙirarin da masu ƙoƙarin faɗar ƙarya don ruɗar da ‘yan Nijeriya.

Kwankwaso ya ce, “wawayen mutane” ne kaɗai za su yarda da zargin cewa yana taimaka wa Tinubu a ɓoye, inda ya tirje akan cewa tawagar siyasarsa ta duƙufa ne kaɗai wajen yi wa Jam’iyyar NDC hidima.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Global a ranar Laraba, inda ya bayar da amsa ga kalaman Sanusi Bature Dawakin Tofa, wato Kakakin Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf.

Bature ya yi zargin cewa Kwankwaso, ya yi wa Tinubu aiki hatta a zaɓen 2023 kuma a kwanan nan ya nemi ganawa da shugaban ƙasar, saidai ganawar ba ta kasance ba.

Akan haka ne Kwankwaso ya ce babu wani shirin siyasa da aka ƙulla tsakaninsa da shugaban ƙasar.

Saidai duk da haka, Kwankwaso ya tabbatar da kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da Tinubu, inda ya ce har yanzu shugaban wa ne a gare shi kuma aboki, yana mai cewa hakan ba shi ke nuna alaƙar siyasa ba.

Tsohon ministan tsaron ya kuma zargi manyan jami’an gwamnatin da ke kewaye da Tinubu da cewa su ne masu hana ruwa gudu a ƙasar wajen ɓoyewa shugaban haƙiƙanin halin da ƙasar take ciki.

Har ila yau, ya yi zargin mutane da dama da ke kusa da shugaban suna da alhakin taɓarɓarewar matsalolin Nijeriya a madadin su taimaka a warware su.

By Babaji