Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Aƙalla mata 15,000 ne ake sa ran za su samu horo kan ilimin amfani da fasahar zamani, tsaro da tsabtace amfani da yanar gizo domin cike giɓin da ke ƙara faɗaɗa tsakanin Arewacin Najeriya da sauran sassan ƙasar nan a wannan zamani na ci gaban fasahar sadarwa.
Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma Centre for Information Technology Development (CITAD) ta bayyana cewa horaswar ta zama wajibi duba da yadda yankin Arewa ke ci baya a ɓangaren fasahar sadarwa da bayanai (ICT), wanda babu wata gagarumar cigaba da za a samu ba tare da shi ba.
Babban Daraktan CITAD, Y.Z. Ya’u, wanda Isa Garba ya wakilta, ya ce manufar horaswar ita ce rage giɓin da ake samu a bangaren fasahar zamani a duniya mai tafiya da ICT.
“Kasuwannin da ke tafiya da fasahar sadarwa ta ICT wanda a yanzu a kan titi guda a Legas sun fi dukkan kasuwannin ICT da ke Kano yawa. Yayin da mutanen Legas suka riga suka kai ga tudun mun tsira, mu kuwa yanzu muka fara tafiya a harkar ICT. Wannan ne ya sa muka ƙuduri aniyar horas da mata 15,000 domin rage giɓin fasahar zamani,” in ji shi.
Ya’u ya ƙara da cewa wajibi ne a bai wa mata damar koyon fasahar zamani domin bunƙasa rayuwar tattalin arziki da zamantakewar al’umma, tare da tasiri mai amfani ga dukkan ɓangarorin rayuwa.
Manajan aikin horaswar ilimin fasahar zamani ta CITAD Fatima Babakura, ta bayyana cewa za a horas da kusan mata da ƴan mata 5,000 masu shekaru tsakanin 16 zuwa 40 harkokin kasuwanci ta yanar gizo domin su anfana da damar samun kuɗaɗen shiga a duniyar zamani.
“Har ila yau da mu wayar da kan mata kan yadda za su kare kansu daga cin zarafi ta yanar gizo da hare-haren masu kutse a yanar gizo domin su koma al’ummominsu su yaɗa ilimin da suka samu.
“Sannan muna kuma horas da ɗalibai kan jarabawar CBT saboda mun gano cewa da dama suna faɗuwa jarabawa ne saboda rashin ƙwarewar amfani da kwamfuta,” in ji Babakura.
Daraktan ICT na hukumar makarantun sakandare ta Jihar Kano (KSSB), Isyaku Garba, ya ce hukumar ta tsara shirye-shirye na musamman domin bai wa ɗalibai ilimin ICT yadda za su iya gogayya da takwarorinsu a ko’ina cikin duniya.
Ya ce tun a shekarar 2006 jihar Legas ta kai sama da kashi 60 cikin 100 na anfani da kayayyakin ICT, tare da dumbin mata masu ilimin fasahar zamani.
Daraktan ya kara da cewa mata masu ilimin zamani na iya yin aiki daga gidajensu na aure, lamarin da zai rage wa mazajensu nauyin tattalin arziki.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka zaɓa domin samun horaswar, Fiddausi Nasir Sulaiman, ta ce ta samu hanyar neman shiga shirin ne ta yanar gizo, daga baya kuma aka sanar da ita cewa an zaɓe ta cikin waɗanda za su amfana.
Ta bayyana cewa ilimin fasahar zamani ya zama abu mai muhimmanci da tasiri a duniya ta yau, tana mai cewa a shirye take ta samu kwarewa ta musamman da za ta buɗe mata damarmaki ba kawai a Kano ba har ma da sauran sassan kasar nan.
