
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar mazaɓar Gwale, Abdulmajid Mai Rigar Fata ya fice daga jam’iyyar APC, tare da sanar da komawarsa zuwa NDC.
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NDC, Rabiu Musa Kwankwaso ne ya tarɓe shi a gidansa da ke Maitama a Birnin Tarayya Abuja, ranar Alhamis.
Mai taimaka wa Kwankwaso akan harkokin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan ya bayyana hakan ta shafinsa na Facebook, inda ya ce tare da Mai Rigar Fata akwai tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Kabiru Sani Auwal Obi, da Mahadi Isa Umar, waɗanda suma suka shiga NDC.
Rahotanni sun ce, Mai Rigar Fata ya sauya sheƙa ne bayan ya kasa samun tikitin APC domin sake tsayawa takarar kujerarsa a zaɓen gaba.
Kafin haka, an zaɓe shi ɗan majalisa a 2023 ƙarƙashin jam’iyyar NNPP kana daga bisani ya koma APC tare da gwamna Abba Kabir Yusuf.
Wannan mataki na zuwa ne bayan wata kotun tarayya ta buɗe ƙofa ga ’yan siyasa masu son koma wa wasu jam’iyyu domin tsayawa takara a babban zaɓen 2027.
