
Hon. Kingsley Ogundu Chinda, wanda ake ganin na hannun dama ne ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya zama ɗan takarar gwamnan jihar Ribas a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC.
Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwani na APC, Bitrus Kwamoti ne ya sanar da hakan a Fatakwal, babban birnin jihar bayan tattara sakamakon zaɓen daga ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Kwamoti ya ce Chinda, wanda shi kaɗai ya tsaya takara a zaɓen, ya samu jimillar ƙuri’u 268,497.
Ya bayyana cewa, Chinda ya cika dukkan sharuɗɗan kundin tsarin APC da ƙa’idojin jam’iyyar, saboda haka aka ayyana shi a matsayin ɗan takarar gwamna na APC a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa sauran masu neman takarar, ciki har da Gwamna Siminalayi Fubara, sun janye daga zaɓen fidda gwanin kafin gudanar da shi.
