
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja, ta soke wasu muhimman ƙa’idoji da Hukumar Zaɓe (INEC) ta gindaya yayin shirin babban zaɓen 2027 a Nijeriya.
Daga ciki akwai tilasta wa jam’iyyun siyasa gabatar da cikakken rajistar mambobinsu kafin 10 ga Mayu, 2026 domin shiga zaɓen 2027.
Mai Shari’a M.G. Umar ya yanke hukuncin wannan ne bayan ƙarar da jam’iyyar YP, wato Youth Party da wasu suka shigar na ƙalubalantar tsauraran jaddawalin da INEC ta fitar.
Akan haka ne kotun ta ba wa jam’iyyun siyasa sabon wa’adi zuwa Satumba, 2026 domin gabatar da sabunta rajistar mambobinsu.
Haka kuma, hukuncin ya tsawaita wa’adin da ya shafi zaɓen fidda gwani da gabatar da sunayen ‘yan takara, sakamakon cewa INEC ba ta da hurumin sanya wa jam’iyyun wa’adi akan haka.
Ana ganin wannan hukuncin a matsayin abin da zai ba wa jam’iyyu ƙarin lokaci wajen sasanta rikice-rikicen cikin gida da kuma karɓar masu sauya sheƙa kafin kulle rajista.
Wannan na nufin hukuncin ya bai wa jam’iyyu damar cigaba da harkokin rajistarsu har zuwa watan Satumba.
