
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da rahoton da ya karaɗe kafafen sadarwa cewa Shugaba Bola Tinubu ya shirya yi wa dokar ƙasa gyara domin sauya sunan Nijeriya zuwa “United States of Nigeria” da kuma soke shari’ar Musulunci a arewacin Nijeriya, tana mai bayyana shi a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma.
A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a ranar Alhamis, fadar ta ce labarin wanda ya ras tushe, wani ɓangare ne na yunƙurin haifar da rikicin siyasa da rashin amincewar ‘yan ƙasa akan jagorori daga wasu ‘yan siyasa domin hana ruwa gudu yayin tunkarar babban zaɓen 2027.
Akan haka ne fadar ta roƙi jama’a da su yi watsi da rahoton baki ɗayansa, tana mai gargaɗin cewa waɗanda suka ƙagi labarin Wakilai ne na tayar da zaune-tsaye.
Haka kuma, ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ba shi da niyyar tura kowane wani ƙudiri ga majalisar dokokin ƙasa mai taken “Project True Federation” a ranar 15 ga Disamba gabanin babban zaɓe.
A cewar sanarwar, gyaran doka ba abu ne da ya ta’allaƙa ba ga shugaban ƙasa ko majalisar dokokin ƙasa, saidai yana buƙatar nazari mai zurfi da zazzafar muhawara gabanin yanke hukuncin sanyawa a doka.
A madadin haka, fadar ta ce Shugaba Tinubu ya mayar da hankalinsa ne aka gyare-gyaren lamuran tattali da ya sanya a gaba da nufin samar da ɗorewa a fannin don amfanin ‘yan Nijeriya.
Kazalika, ta gargaɗi ‘yan Nijeriya akan kiyaye ɗaukar labaran ƙarya da masu rarraba kawunansu, musamman akan lamuran siyasa ganin yadda 2027 ke cigaba da ƙaratowa.
