
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Zakaran ƙwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo ya ci ƙwallaye biyu a wasan da ƙungiyarsa ta Al-Nassr ta yi da Damac, inda aka tashi 4 da 1, lamarin da ya ba su damar lashe kofin Saudi Pro League na kakar 2025/2026.
Wannan al’amari ya nuna Al-Nassr ta lashe kofin har sau 11 a tarihinta kuma ya yi sanadiyyar lashe babban kofi ga Ronaldo tun zuwansa ƙasar a 2023.
Haka kuma nasarar ta kawo ƙarshen rashin nasarar lashe kofi a matakin cikin gida ga ƙungiyar.
Ƙungiyar ta Riyadh ta shiga zangon wasan ƙarshe ne yayin da ta ke ba wa ta biyu a gasar, wato Al-Hilal ratar maki biyu kacal, wands ya sa ya zama wajini ta yi nasara a wasan kafin lashe kofin.
Kocin Al-Nassr, Jorge Jesus ya ce babban dalilin da ya sa shi karɓar aikin jagorantar ƙungiyar shi ne taimaka wa Ronaldo lashe manyan kofuna.
Ƙwallaye biyun na Ronaldo a wasan ƙarshen sun sanya adadin waɗanda ya zura sun haura 100 tun zuwansa ƙungiyar.
