Zaɓukan APC: Wasu sun dara, wasu sun koka

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Zaɓukan fidda gwani na Jam’iyyar ‘All Progressiɓes Congress’ (APC) da aka gudanar a sassa daban-daban na Niijeriya sun bar baya da ƙura, rikice-rikice, koke-koke, zarge-zargen maguɗi da murnar nasara daga ɓangarori mabambanta, yayin da jam’iyyar ke ƙoƙarin tsara dabarun tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Yayin da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar suka samu tikitin takara cikin farin ciki da gagarumar nasara, wasu kuwa sun bayyana zaɓukan a matsayin “wasan kwaikwayo” da aka shirya domin fifita wasu ‘yan takara, lamarin da ya haddasa zanga-zanga da kuma barazanar ɗaukaka ƙorafe-ƙorafe zuwa matakin ƙasa.

A wasu jihohi, an samu tarzoma, yayin da a wasu yankuna dubban magoya bayan jam’iyyar suka mamaye tituna suna nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓukan.

Daga cikin manyan abubuwan da suka fi ɗaukar hankali akwai yadda wasu fitattun sanatoci da tsofaffin gwamnoni suka rasa tikitin takara, yayin da wasu da ke fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa suka samu damar tsallakewa cikin nasara.

A jihar Delta, tsohon gwamna Ifeanyi Okowa ya kayar da Sanata Ned Nwoko a zaɓen Delta ta Arewa, duk da cewa yana fuskantar shari’ar EFCC kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati. Haka kuma a Kogi ta Tsakiya, tsohon gwamna Yahaya Bello ya samu nasara duk da tuhume-tuhumen da yake fuskanta a kotu.

Wannan lamari ya jawo suka daga wasu ‘yan Nijeriya da masu sharhi kan siyasa, waɗanda suka zargi APC da nuna son kai da kuma bai wa masu fuskantar shari’a kariya ta siyasa.

Sai dai duk da cece-kucen, wasu manyan jiga-jigan APC sun samu tikitin takara cikin kwanciyar hankali. Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Mataimakinsa Barau Jibrin, Sanata Ali Ndume, Ahmad Lawan, Orji Uzor Kalu da Opeyemi Bamidele na daga cikin waɗanda suka samu nasara cikin sauƙi ko ta hanyar maslaha.

A jihar Imo kuwa, gwamna Hope Uzodimma ya nuna ƙarfin siyasa bayan da ya kayar da tsohon gwamna Rochas Okorocha da gagarumin rinjaye wajen neman tikitin Imo ta Yamma, lamarin da masana siyasa suka bayyana a matsayin babban sauyi mai matuƙar tasiri a siyasar jihar.

Haka kuma a jihar Gombe, tsohon gwamna kuma sanatan da ya shafe lokaci akan kujerar, Muhammad ɗanjuma Goje ya rasa damar komawa majalisar dattawa karo na biyar bayan shan kaye hannun tsohon jami’in ɗan sanda DCP Ahmad Mohammed Jarman Deba.

Sai dai a gefe guda, rikice-rikice sun fi ƙamari a wasu yankuna inda masu neman takara da magoya bayansu suka yi zargin cewa an rigaya an tsara sakamakon tun kafin a fara kaɗa ƙuri’a.

A jihar Edo, Sanata Neda Imasuen ya yi watsi da sakamakon zaɓen Edo ta Kudu, yana mai cewa magoya bayan wasu ‘yan takara kaɗai aka bari suka shiga wurin zaɓe, yayin da ya zargi shugabannin jam’iyya da shirya sakamakon tun da farko.

A jihar Ondo kuma, harbe-harbe sun tarwatsa masu zaɓe a Akure bayan wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kama harbe-harben bindiga sama, lamarin da ya sa mutane suka riƙa gudu domin tsira da rayukansu.

Sanata Adeniyi Adegbomire ya yi zargin cewa motarsa ta samu harbin bindiga yayin da shi kansa aka yi yunƙurin kai masa hari.

A jihar Adamawa kuwa, dubban magoya bayan APC daga Numan, Demsa da Lamurde sun gudanar da zanga-zanga bayan sanar da Honorabul Kwamati La’ori a matsayin wanda ya lashe tikitin majalisar wakilai.

Masu zanga-zangar sun bayyana sakamakon a matsayin ƙaƙaba musu ɗan takara, inda suka ce babu wani zaɓe da aka gudanar a yankin.

Tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Lamurde, Honorabul ɓrati Nzonzo, ya bayyana abin da ya faru a matsayin cin zarafin dimokuraɗiyya tare da kira ga shugabancin APC na ƙasa da ya soke sakamakon tare da sake gudanar da sabon zaɓe.

Haka kuma wata mai neman takara, Misis Justina Obadiah Nkom, ta ce jami’an yaƙin neman zaɓensu sun jira tsawon lokaci ba tare da ganin jami’in zaɓe ko guda ba.

A jihar Nasarawa ma, wata ƙungiyar APC Concern Group ta bayyana zaɓukan fidda gwani da ake gudanarwa a jihar a matsayin ‘mai cike da maguɗi da rashin adalci’, tana mai zargin cewa an hana magoya bayan wasu ‘yan takara damar kaɗa ƙuri’a cikin ‘yanci.

Shugaban ƙungiyar, Honorabul Abdullahi Yammani, ya ce abin da suka gani a wasu wuraren zaɓe ya nuna cewa an riga an tsara sakamakon tun kafin fara zaɓe.

Duk da koke-koke da rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓukan, shugabannin APC sun ci gaba da jaddada cewa an gudanar da mafi yawan zaɓukan cikin lumana da adalci, tare da bayyana hakan a matsayin wata alama ta haɗin kai da ƙarfin jam’iyyar.

Sai dai masana siyasa na ganin cewa abubuwan da suka faru sun nuna irin ƙalubalen da APC ke fuskanta daga rikicin cikin gida, fafatawar neman muƙami, siyasar maslaha da kuma rashin jituwa tsakanin tsofaffi da sababbin masu tasiri a jam’iyyar.

Yayin da wasu ke murnar nasarar da suka samu, wasu kuma sun fito fili suna nuna ɓacin ransu, suna masu gargaɗin cewa idan ba a sasanta rikice-rikicen cikin gida ba, za su iya yin tasiri ga ƙarfin jam’iyyar a babban zaɓen 2027 mai zuwa.

By ukarofi