Masu more tallafin mai da canjin kuɗaɗe ke haddasa matsalar tsaro – Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya zargi waɗanda suka amfana da tsohon tsarin biyan tallafin man fetur da kuma tsari na farashin canjin kuɗaɗen waje daban-daban da hannu wajen ƙara ta’azzarar matsalar tsaro da yunƙurin tayar da zaune tsaye a Nijeriya bayan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta aiwatar.

Tinubu ya kuma bayyana cewa wasu ƙungiyoyi masu ƙarfin faɗa a ji da suka amfana da damfara a harkar canjin kuɗaɗen waje da cin hanci a tsarin tallafin mai yanzu suna “fatan ya mutu” saboda manufofin da ya ƙaddamar tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne ta bakin tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba, a ranar Laraba yayin ƙaddamar da littafin The NADECO Story wanda Cif Ayo Opadokun ya rubuta, a cibiyar taruka ta Muson Centre da ke Onikan a Legas.

Taron ya kuma hada da karrama wasu fitattun mutane da suka taka muhimmiyar rawa a gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya ƙarƙashin ƙungiyar National Democratic Coalition (NADECO) tsakanin shekarun 1994 zuwa 1998.

A cewar Tinubu, wasu masu ruwa da tsaki da suka fusata saboda cire tallafin mai da haɗa kasuwannin canjin kuɗaden waje zuwa tsari guda suna ƙoƙarin kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Osoba, yayin da yake gabatar da saƙon shugaban ƙasar, ya ce: “Dangane da batun tsaro, shugaban ƙasa ya ce na sanar da ku cewa yana sane da akwai wata manufa ta tayar da zaune tsaye a ƙasar nan daga wasu mutane da ya san sun ji haushinsa saboda soke tsarin farashin dala daban-daban da kuma cire tallafin mai.”

Tinubu ya kuma zargi wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi da ci gaba da gudanar da damfara ta hanyar anfani da giɓin canjin kuɗaɗen waje duk da sauye-sauyen da aka yi.

“Waɗannan ƙungiyoyi masu anfani da tsarin canjin kuɗi suna iya fatan ya mutu a kowane lokaci, amma ya ƙuduri aniyar cewa ko wannan ne kaɗai zai yi, zai tabbatar da ya sake fasalin tattalin arzikin ƙasa. Duk da komai, ya shirya fuskantar hakan,” inji Osoba.

Tinubu ya bayyana tattalin arziki da tsaro a matsayin manyan ƙalubalen da suka fi damun gwamnatinsa a yanzu, yana mai cewa waɗannan fannoni ne suka fi buƙatar cikakken hankalinsa.

Ya ce, bayan an samu daidaito a tattalin arziki da kuma inganta tsaro, gwamnatin za ta fara duba sauran muhimman batutuwan siyasa.

“Kullum yana cikin godiya Allah…” Osoba ya ce shugaban ƙasar ya bayyana godiyarsa ga duk waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen kai Nijeriya inda take a yau, tare da alƙawarin cewa idan ya samu wa’adi na biyu, zai fara aiwatar da wasu daga cikin batutuwan siyasa da ake buƙata.

Shugaban ƙasar ya kuma nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke fara yaɗuwa zuwa yankin Kudu maso Yammacin Nijeriya.

“Kowa na iya gani yanzu cewa matsalar tsaro tana fara kutsawa sannu a hankali zuwa yankin Kudu maso Yamma,” Osoba ya faɗa yana ambaton kalaman Tinubu.

Dangane da tattalin arziki kuwa, Tinubu ya kare tsarin haɗa kasuwannin canjin kuɗaɗen waje, yana mai cewa hakan ya rage babban giɓi tsakanin farashin dala na kasuwar gwamnati da ta bayan fage.

“Bambancin da ke tsakanin kasuwar bayan fage da ta hukuma kusan ya zama sifili yanzu. Naira da mutane suka yi hasashen za ta kai N2,000 kan dala ɗaya, yanzu tana kusan N1,380 ko makamancin haka,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa ba ya son naira ta yi ƙarfi fiye da kima ta yadda hakan zai haifar da tangarɗa a tattalin arziki.

“A gaskiya, ba zai bari naira ta yi ƙarfi sosai ba. Ba ya son ya haifar da ruɗani ga waɗanda suka sayi dala a kan N1,500 da sauran kayayyaki,” Osoba ya ƙara da cewa.

Tinubu ya yaba wa mambobin NADECO bisa sadaukarwar da suka yi a gwagwarmayar dimokuraɗiyya a Nijeriya, yana mai cewa gudunmawarsu ce ta shimfiɗa tubalin tsarin dimokuraɗiyyar da ake da shi yanzu.

A cewar Osoba, shugaban ƙasar ya amince cewa ba zai kai matsayin shugaban ƙasa ba da ba don taimako da gudunmawar tsofaffin jagororin NADECO ba.

“Shugaban ƙasa ya ce in gaya muku cewa yana tare da ku gaba ɗaya, kuma yana da matuƙar girmama ku saboda ba zai kai inda yake a yau ba da ba domin gwagwarmayar da kuka yi wajen tabbatar da dimokuraɗiyya ba,” inji Osoba.

Tinubu ya kuma tabbatar wa magoya bayansa cewa zai yi aiki fiye da yadda yake yi yanzu idan aka sake zaɓensa karo na biyu.

By ukarofi