2027: Masu sharhi sun yi hasashen takarar Tinubu/Shettima, Atiku/Amaechi, Jonathan/Lamido da Obi/Kwankwaso

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Masu sharhin siyasa na matakin ƙasa sun fara hasashen yadda manyan jam’iyyun siyasa za su fito da tikitin takarar shugaban ƙasa da mataimaki a zaɓen 2027.

A cewar masu sharhin, ana hasashen APC za ta sake tsayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Mataimakinsa Kashim Shettima, yayin da PDP za ta iya fito da tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan tare da Sule Lamiɗo.

Haka kuma an yi hasashen cewa jam’iyyar NDC za ta iya tsayar da Peter Obi tare da Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da ADC za ta iya bai wa Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi tikiti.

A wani ɓangare kuma, ana ganin APM na iya fito da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, tare da gwamnan Bauchi Bala Mohammed.

Masu sharhin sun bayyana cewa waɗannan hasashe sun samo asali ne daga tattaunawa, haɗaka da motsin siyasar da ake gani a tsakanin manyan ‘yan siyasa gabanin zaɓen fidda gwani na jam’iyyu.

Sai dai sun jaddada cewa babu wata jam’iyya da ta gudanar ko ta kammala zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa zuwa yanzu, don haka dukkan haɗakar da ake magana a kai hasashe ne kawai.

Masana siyasar sun kuma lura cewa jam’iyyun adawa sun rabu gida-gida, lamarin da ka iya bai wa APC da Shugaba Tinubu damar cin gajiyar rabuwar ƙuri’u a 2027.

Sun ce idan manyan ‘yan takara suka fito daga jam’iyyu daban-daban, ƙuri’u za su watse sosai, wanda hakan zai iya sa bambancin nasara ya kasance ƙanƙani tsakanin wanda ya yi nasara da sauran ‘yan takara.

By ukarofi