Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da kammala jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya, domin gudanar da aikin Hajjin 2026 akan kari.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis, ta bayyana cewa an fara jigilar maniyyatan ne tun ranar 3 ga Mayu, 2026, sannan aka kammala aikin da jirgin Maɗ Air na ƙarshe da ya ɗauki maniyyatan jihar Zamfara daga filin jirgin saman Gusau.
NAHCON ta ce an gudanar da jimillar jirage 98 cikin kwanaki 18, inda ake gudanar da kusan jirage biyar a kullum yayin aikin jigilar.
Nijeriya ta samu kujerun maniyyata 50,000 domin aikin Hajjin bana, ciki har da kujeru 9,750 da aka ware wa kamfanonin yawon Hajji masu lasisi, jami’an aiki da sauran hukumomin gwamnati.
Hukumar ta bayyana cewa kimanin maniyyata 39,000 karkashin tsarin gwamnati ne aka yi nasarar jigilar su zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji, ba tare da ƙirga jami’ai da wakilan gwamnati ba.
Sai dai NAHCON ta ce wasu daga cikin masu niyyar tafiya sun kasa samun damar zuwa ne sakamakon wasu matsaloli da suka haɗa da rashin lafiya da kuma rasuwa bayan kammala biza.
Shugaban hukumar, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya yaba da hadin kai da jajircewar ma’aikatan hukumar, hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, jami’an tsaro, kamfanonin jiragen sama da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da nasarar aikin jigilar.
Hukumar ta kuma yabawa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima bisa goyon bayan da suka bayar domin tabbatar da lafiyar da jin daɗin maniyyatan Nijeriya.
A ƙarshe, NAHCON ta bayyana cewa tana kammala shirye-shiryen dawo da maniyyata gida, wanda ake sa ran zai fara daga ranar 3 ga Yuni, 2026.
