2027: Dan uwan Fubara ya sayi fom ɗin takarar gwamna a NDC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Sa’o’i kaɗan bayan gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara, ya janye daga takarar gwamnan jihar a zaɓen shekarar 2027, wani ɗan siyasa mai ɗauke da sunan Fubara ya shiga fafatawar neman kujerar ƙarƙashin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC).

Sabon ɗan takarar, mai suna Blessing Fubara Snr., ya karɓi fom ɗin tsayawa takara da nuna sha’awa na jam’iyyar domin neman kujerar gwamnan jihar Ribas a zaɓen 2027.

Blessing Fubara ya karɓi fom ɗin ne a hedikwatar jam’iyyar NDC ta ƙasa da ke Abuja ranar Laraba, lamarin da ya sake tayar da sabon zance a siyasar jihar Ribas bayan janyewar ba-zata da gwamna Siminalayi Fubara ya yi daga takarar.

Sabon sauyi ya ja hankalin masu bibiyar siyasa

Ko da yake Blessing Fubara da Gwamna Siminalayi Fubara duk sun fito ne daga ƙaramar hukumar Opobo/Nkoro ta jihar Ribas, har yanzu ba a tabbatar da ko suna da alaƙar jini kai tsaye ba.

Shugaban Jam’iyyar NDC na jihar Ribas, Honorabul Success Jack, ya tabbatar da cewa Blessing Fubara na daga cikin masu neman tikitin gwamna na jam’iyyar, sai dai ya ce bai da tabbacin ko akwai alaƙar iyali tsakaninsa da gwamnan jihar.

“Eh, ya karɓi fom ɗin nuna sha’awa jiya a Abuja, kuma muna ci gaba da shirye-shiryen lashe ba kawai zaɓen gwamna ba, har ma da dukkan zaɓukan jihar Ribas a shekarar 2027,” in ji shugaban jam’iyyar.

Tsoffin mambobin APC sun koma NDC

Rahotanni sun nuna cewa Blessing Fubara ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa NDC kimanin makonni biyu da suka gabata.

A lokacin da ya sauya shekar a Abuja, shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, tare da wasu masu ruwa da tsaki ne suka tarbe shi.

A wajen taron, an rawaito Blessing Fubara yana bayyana NDC a matsayin “jirgin ƙasa mai tafiya,” yana mai cewa shawarar da ya yanke ta shiga jam’iyyar ta samo asali ne daga muradin al’ummar jihar Ribas.

Ya kuma bayyana cewa “makomar jihar Ribas na cikin haɗari” yayin da sauye-sauyen siyasa ke ci gaba da ƙara zafi gabanin zaɓen 2027.

ɗan takarar ya bayyana ƙwarewarsa

Blessing Fubara Snr. na da digiri a fannin Community Deɓelopment and Adult Education, sannan a halin yanzu shi ne Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin D’Consiglories LLC.

Ana kuma bayyana shi a matsayin cewa masani ne kan dabarun ci gaban al’umma, gyaran birane da tattara goyon bayan jama’a, tare da gogewa wajen bayar da shawarwari a ɓangaren gwamnati da shirye-shiryen ƙarfafa matasa.

Fitowarsa takara ta riga ta fara jawo martani mabambanta a siyasar jihar Ribas.

Yayin da magoya bayan NDC ke kallon takararsa a matsayin wani sabon yunƙuri da zai iya sauya yanayin siyasar adawa a jihar, masu sukar lamarin na ganin babban ƙalubalen jam’iyyar shi ne yadda za ta gina ƙaƙƙarfan tsari a faɗin jihar domin fafatawa da manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya a zaɓen 2027.

By ukarofi