Yadda shanun da aka sace suka gano masu su a tsakiyar kasuwa

Spread the love

An shiga ruɗani da tashin hankali a kasuwar Ajase-Ipo da ke ƙaramar hukumar Ifelodun a jihar Kwara, bayan wasu shanu guda biyar da ake zargin an sace su sun gano masu su tare da tona asirin wani da ake zargi da safararsu.

Lamarin ya faru ne a ranar 11 ga watan Janairun 2026 yayin da kasuwar ke shirin rufewa da yamma. Rahotanni sun ce wani mutum ya kawo shanun cikin sirri domin sayar da su ba tare da ya ja hankali ba.

Sai dai abin mamaki ya faru ne lokacin da shanun suka hangi makiyayan da suka saba da su daga cikin taron jama’a.

Shaidu sun ce nan take shanun suka rikice, suka fara jan igiyoyinsu tare da ƙoƙarin zuwa wajen makiyayan, yayin da suka fara fizga da ƙarfi tamkar suna neman agaji.

Wannan lamari ya sa masu saye da sayarwa suka tsaya cak domin kallon abin da ke faruwa.

Wani ɗan kasuwa a kasuwar mai suna Danjuma Bature ya ce abin ya ba mutane mamaki saboda tun kafin makiyayan su yi iƙirarin mallakar shanun, dabbobin ne suka fara gane masu su.

Ya ce, “Shanu ba sa mantawa da mutanen da ke ciyar da su da kula da su kullum. Suna gane murya, fuska da halayen masu su.”

Daga nan ne makiyayan suka matsa gaba suna bayyana alamomin da suka tabbatar musu cewa shanun nasu ne, ciki har da siffofin ƙaho, tabo da raunukan da ke jikin dabbobin.

Bayan haka hankalin jama’a ya koma kan mutumin da ya kawo shanun kasuwa, wanda aka bayyana sunansa da Mohammed Jabi mai shekara 30 daga ƙauyen Buju na jihar Neja, amma mazaunin Patigi a jihar Kwara.

Rahotanni sun ce lokacin da aka tambaye shi yadda ya samu shanun, ya kasa bayar da gamsasshiyar amsa, lamarin da ya sa jami’an kasuwa suka kira Rundunar Musamman da Sufeto Janar na ’Yan Sanda na ƙasa, Olatunji Disu, ya kafa domin yaƙi da miyagun laifuka.

Masu bincike sun ce ana zargin Mohammed Jabi na aiki ne ƙarƙashin jagorancin wani shugaban ’yan bindiga mai suna Bachujo, wanda ake zargin yana da alaƙa da wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da satar shanu da ke aiki a dazukan jihohin Kwara, Neja da Kogi.

Rahoton ya ce sakamakon matsin lambar hare-haren jami’an tsaro a dazuka, ana zargin ƙungiyar ta fara tura shanun da aka sata kasuwanni domin sayarwa tare da samun kuɗin sayen abinci da kayan aiki.

A halin yanzu, jami’an tsaro sun tsare Mohammed Jabi, yayin da aka mayar da shanun ga masu su.

Jami’an tsaro sun kuma bayyana cewa suna ci gaba da farautar sauran mambobin ƙungiyar.

Mutanen da suka shaida abin sun ce darasin da suka koya shi ne cewa mutum na iya yaudarar mutane, amma dabbar da ta san mai kula da ita ba za a iya ruɗarta cikin sauƙi ba.

By ukarofi