NUT ta gudanar da zanga-zanga a jihohi da dama kan malamai da ɗaliban da aka sace

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kungiyar Malaman Makarantu ta Nijeriya (NUT) ta gudanar da zanga-zangar lumana a jihohi da dama na ƙasar nan domin nuna damuwa kan ci gaba da tsare malamai da ɗaliban da aka sace a Jihar Oyo.

Rahotanni sun nuna cewa zanga-zangar ta biyo bayan irin wadda ƙungiyoyin farar hula suka gudanar a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, inda suka buƙaci a gaggauta ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

A Ibadan, malamai sun taru a harabar ofishin Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) da ke yankin American ƙuarter, inda shugabannin ƙungiyar suka yi musu bayani kan dalilin gudanar da gangamin.

Bayan haka, masu zanga-zangar sun yi jerin gwano ta wasu sassan birnin dauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban da ke nuna damuwarsu, yayin da suke rera wakokin haɗin kai tare da wayar da kan jama’a game da halin da suke ciki.

Shugabannin ƙungiyar sun jaddada cewa gangamin ba na rikici ba ne, illa kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakin gaggawa domin ceto waɗanda aka sace.

A Jihar Filato kuwa, malamai sun bayyana cewa sace malamai da ɗalibai barazana ce ga harkar ilimi a Nijeriya.

Da yake jawabi ga masu zanga-zangar a Jos, shugaban NUT na Jihar Filato, Elisha Ayimani, ya ce yawaitar hare-haren da ake kai wa makarantu da malamai na iya jefa makomar ilimi cikin haɗari.

Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa domin tabbatar da sakin waɗanda aka yi garkuwa da su.

Ayimani ya kuma bayyana cewa ƙungiyar za ta ci gaba da matsa lamba har sai an kuɓutar da malamai da ɗaliban tare da haɗa su da iyalansu.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki daga Old Airport Roundabout zuwa Sabon Gidan Gwamnati da ke Little Rayfield, inda suka shirya miƙa takardar koke ga Gwamna Caleb Mutfwang.

NUT ta ce tabbatar da tsaron malamai da ɗalibai abu ne mai matuƙar muhimmanci domin kare makomar ilimi a Nijeriya.

An gudanar da irin wannan zanga-zanga a wasu jihohin ƙasar ciki har da Kano, yayin da malamai ke ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su gaggauta ɗaukar matakin ceto waɗanda ke hannun masu garkuwa da mutane.

By ukarofi