FIFA ta tabbatar da sabbin dokokin Gasar Kofin Duniya ta 2026

Spread the love

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA) ta tabbatar da wasu sabbin dokoki da za su fara aiki a Gasar Kofin Duniya ta 2026, matakin da ake sa ran zai taimaka wajen rage ɓata lokaci, ƙara gaskiya a yanke hukunci da kuma inganta tafiyar da wasa.

Daga cikin manyan sauye-sauyen da aka amince da su akwai sanya iyaka ga lokacin da ‘yan wasa za su ɗauka wajen dawo da ƙwallo cikin wasa, canje-canjen ‘yan wasa, da kuma ƙarin amfani da fasahar Bidiyon Taimaka wa Alƙali (VAR).

Sabuwar dokar jefa ƙwallo daga gefe ta tanadi cewa idan ɗan wasa ya yi gangancin jinkirta dawo da wasa, dole ne ya jefa ƙwallon cikin daƙiƙa biyar. Idan ya gaza yin hakan, za a bai wa abokan hamayya damar jefa ƙwallon.

Haka kuma, a lokacin bugun daga raga, mai tsaron gida ko ‘yan wasa ba za su iya ɓata lokaci ba. Dole ne a dawo da wasa cikin daƙiƙa biyar, in ba haka ba za a bai wa abokan hamayya bugun kusurwa.

A bangaren canjin ‘yan wasa kuwa, FIFA ta ƙayyade cewa ɗan wasan da aka cire daga wasa dole ne ya fita daga filin wasa cikin daƙiƙa 10 ta hanyar mafi kusa. Idan ya ƙi ko ya yi jinkiri, sabon ɗan wasan ba zai shiga filin ba sai bayan minti ɗaya, yayin da ƙungiyarsa za ta ci gaba da wasa da ‘yan wasa 10 kacal a wannan lokacin.

Sabuwar dokar kula da rauni kuma ta tanadi cewa duk ɗan wasan da jami’an lafiya suka yi wa magani a cikin fili dole ne ya kasance a wajen fili na tsawon daƙiƙa 60 kafin ya dawo wasa. Sai dai an ware wasu lokuta na musamman, kamar idan mai tsaron gida ne, ko kuma idan an ba abokin hamayya kati saboda laifin da ya haddasa raunin.

FIFA ta kuma yi gargaɗi kan halin da wasu ‘yan wasa ke nunawa yayin gardama a fili. Sabuwar doka ta ce duk ɗan wasan da ya rufe bakinsa da hannu yayin muhawara ko gardama da abokin hamayya na iya fuskantar jan kati idan alƙali ya ga hakan ya dace.

A fannin fasahar VAR, an ba da damar duba hukuncin bugun kusurwa domin tabbatar da cewa an bayar da shi yadda ya kamata. Sai dai wannan binciken dole ne ya kasance cikin sauri kuma kafin a sake fara wasa.

Bugu da ƙari, idan an kori ɗan wasa bayan samun katin gargadi biyu, za a iya sake nazarin katin na biyu ta hanyar VAR domin tabbatar da daidaiton hukuncin. Sai dai ba za a riƙa yin nazari kan yiwuwar bayar da katin gargaɗi na biyu ba kafin a nuna shi.

Ana sa ran waɗannan sababbin dokoki za su taimaka wajen rage ɓata lokaci a filin wasa, ƙarfafa gaskiya a hukunci da kuma sa wasanni su kasance masu kayatarwa da adalci yayin Gasar Kofin Duniya ta 2026.

By ukarofi