Rikicin manoma da makiyaya ya yi ajalin mutum 7 da raunata 6 a Bauchi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin mutane bakwai ne suka rasu da kuma jikkata da wasu shida suka yi bayan ɓarkewar wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyukan Lanzai da Dosho da ke Ƙaramar Hukumar Darazo a Jihar Bauchi.

Rundunar ‘Yan Sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce rikicin ya kuma yi sanadiyyar lalata gidaje da wasu kadarori a ƙauyukan.

A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’ar Rundunar, SP Nafi’u Habib ya fitar a ranar Alhamis, ya ce, hukumar ta samu kira na gaggawa akan farmakin a ranar Litinin da misalin ƙarfe 9:20 na safe.

A cewar ‘yan sanda, rikicin ya faro ne a lokacin da aka yi zargin wasu makiyaya sun farmaki manoma da ke aikin sanya taki a gonarsu da ke wajen ƙauyen Lanzai.

SP Habib ya bayyana cewa, rikicin ya haddasa firgici acikin jama’ar yankin da kuma tunzura wasu mazauna yankin.

A cewarsa, cikin hanzari hukumomin tsaro suka ɗauki mataki yayin da suka samu labarin al’amarin.

Akan harin makiyayan ne wasu matasa daga Lanzai suka mayar da martani a ƙauyen Dosho inda galibin mazauna yankin ‘yan ƙabilar Fulani ne.

A yayin haka, an ƙona gidaje da dama da kuma lalata wasu kadarori, wanda kuma ya haifar da mutuwar mutane bakwai da raunata wasu shida da a yanzu suna halin karɓar magani.

A sakamakon haka, rundunar ‘yan sanda ta tura jami’ai na musamman domin kwantar da hankula da kuma ƙaddamar da bincike akan al’amarin.

By Babaji