‘Yan sanda sun kama motoci bayan dokar haramcin amfani da gilashi mai duhu a Abuja ta fara aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda a Abuja ta cafke sama da motoci 30 bisa saɓa wa dokar amfani da gilashi mai duhu a wani yanayi na tabbatar da bin doka da oda acikin masu amfani da ababen hawa.

Haka kuma, ta kama waɗanda suke ɗauke da allon lambobin da aka sakaya bayanansu da masu rajistar da ba ta cika ƙa’ida ba a babban birnin tarayyar.

Da yake ganawa da manema labarai, Kwamishinan ‘Yan sandan Abuja, Ahmed Sanusi, ya ce an ƙaddamar da atisayen kamen ne da nufin daƙile damar amfani da gilashi mai duhu acikin masu ayyukan garkuwa, fashi ta one-chance da wasu munanan laifuka a birnin.

A cewarsa, Sufeto Janar na hukumar, Olatunji Disu ne ya umarci hukumar da ta tabbatar da fara aiwatar da aiki da dokar taƙaice amfani da irin gilashin.

Ya bayyana cewa, bayyanan sirri da rundunar ta tattara sun nuna cewa ana aikata manyan laifuka ne sau da dama da motoci masu gilashi mai duhu da ɓoyayyun allunan lambobi domin ɓoye kai ga masu yi da guje wa bin diddiginsu gami da haifar da cikas ga ƙoƙarin tabbatar da aiwatar da dokar.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, hakan na zuwa ne bayan umarnin tabbatar da bin dokar haramta amfani da gilashi mai duhu da wasu dokokin tuƙi akan titina da ka iya taimaka wa aikata manyan laifuka acikin al’umma.

By Babaji

Leave a Reply